“Na fuskanci ƙalubale musamman na sare min gwiwa da mutane ke yi”
Daga AISHA ASAS
(Ci gaba daga makon jiya)
MANHAJA: Kowanne abu yana da tsari da kuma matakalai da ake bi don ganin an kai ga nasara, musamman ma harkar irin wannan ta ilimi. Shin waɗanne matakai ne aka taka don ganin wannan aiki ya kai ga nasara?
SADAR: Gaskiya ne shi ya sa tashin farko dana kammala wannan aikin na yi ƙoƙarin kauce wa ‘media’ ko yanar gizo, saboda a wannan lokacin bani da tabbacin me mutane za su faɗa akai, sai na fara haɗa kwamiti na mutane guda bakwai, waɗanda zanyi aiki da su ta ɓangaren samun nasarar wannan aikin kuma a kwamitin aka naɗa shugabanci da sauran matakan da ya kamata wanda har yanzu kwamitin shekarar sa biyu kenan yana nan yana aiki, bayan kafa kwamitin da ni da su sai muka maida hankali wajen gudanar da tafiyar bisa tsari wanda duk abin da za’ayi mai muhimmanci sai an tattauna akan shi, haka muka ci gaba da tafiya muna tuntuɓar maluman mu masana musamman waɗanda suke ɓangaren, kuma alhamdu lillah a wannan tuntuɓar da muke yi mun samu nasarori da dama ta samun shawarwari masu kyau don ƙara inganta al’amarin da kuma samun goyon baya da ƙwarin gwiwa akan ka da na sare da abin da nake yi duk rintsi na daure na ci gaba, haka muke ta tafiya har kawo yanzu.
Sannan mun taka matakai da dama na ganin nasara a wannan al’amari na wannan sabon rubutu abinki da harka ta ilimi wajibi ne sai an zurfaffan bincike duk inda ka shiga ka ke son a ba ka goyon baya akai, domin ganin tabbatuwar kyawun aikin, banda ɗai-ɗaikun malamai da muke ziyarta, mun ziyarci jami’oi da hukumomi na ilimi domin gyara ko shawara kuma alhamdu lillah ana samun cikakken goyon baya da shawarwari wanda babbar nasara da muka samu ita ce, lokacin da na rubuta wa hukumar ilimi ta Kano wasiƙa game da abin da nake yi da kuma abin da nake gani za’ayi, ban yi aune ba, ba wayan wasu lokuta sai na ji kira daga wata hukuma da ke ƙarkashin ta ilimi da ake kira da KERD, bayan na je suka min tambayoyi akan wannan al’amari. To daga nan al’amarin ya ɗora mukai tabin matakai tare da su don ganin an yi abin cikin inganci a hukumance, muna aiki tare da su sai suka turawa jami’ar Bayero da wasiƙa tare da ‘document’ na baƙaƙen da lambobi, domin su yi nazari akai kuma su ba wa gwamnati shawara akai, bayan wani lokaci jami’a ta dawo wa da gwamnati amsar wasiƙar da ta tura mata cike da karɓuwa da kuma gwala-gwalan kalmomi da kuma shawarwari guda uku zuwa huɗu, suka nuna min hanyar da zan bi dan na ƙara ingancin ilimin rubutun, ya zamo yabzauna da ƙafarsa kamar yadda kowanne ilimin rubutu yake a duniya.
Wannan ba ƙaramin farin ciki ya saka ni ba, ganin yadda har jami’a ta yi na’am da wannan al’amari har kuma ta bani shawarwari don ganin an ƙara inganta ilimin, wanda kowa ya sani jami’a ba ta yin abu da ka, sai ta yi bincike sosai kafin ta yarda da kowane al’amari musamman ɓangaren ilimi sabo irin wannan. Gaskiya na ji daɗi, na yi alfahari da hakan, domin wannan ba ƙaramar nasara ba ce ga al’ummar Hausa, sai dai mu ƙara gode wa Allah (S.W.A) wanda har yanzu muna nan muna aiki da hukumar ilimi da kuma jami’a don yanzu haka akwai littattafai da nake rubutawa wanda jami’a ta bani shawarar na samar da su da zarar na yi gyaran da ta bani shawara akai kuma littattafan sun ƙunshin yadda ake koyan ilimin rubutun a sauƙaklƙe da kuma litattafai na ɗalibai, wanda da zarar na kammala su in sha Allah muke sa rai za a nazarce su, sannan a fara koyar da ilimin a makarantun gwamnati, wannan ma ba ƙaramar nasara ba ce da al’ummar Hausa ta samu.
Ta wacce hanya ka ke ganin za su iya samun karɓuwa ga mutane?
Ta hanyoyi da dama, misali akwai hanyoyin sadarwa na zamani da muke da su yanzu wanda waɗannan hanyoyin suna daga mafi sauƙin isar da saƙo zuwa ga al’umma, daga ciki akwai wannan hanyar da muke magana da ke ta jarida, ita ma hanya ce me sauƙi da wasu waɗanda muke shiryawa don ganin an samu sauƙi wajen fahimtar da mutane har su karɓe su, kwananan akwai tashar mu ta YouTube da muka buɗe me suna “MuryarHausaAcademy” wannan tasha za ta bada gudunmmawa wajen nusar da al’umma aikin da muke yi a haka za mu bi matakai da har al’umma za su samu ilimin rubutun idan mutum ya maida hankali shima sai ya ƙware har ya koyar da wasu nan gaba. Za mu nemi ko muna neman haɗaka da ƙungiyoyin marubuta, da na yanar gizo da kuma gidan jaridu irin naku da na talabijin da kuma radiyo da sanar da al’umma mahimmanci wannan rubutu dama yadda ake koyar da shi. Wannan kaɗan kenan daga yadda za mu bi ko muke bi don karɓuwar wannan rubutu ga al’ummar Hausa.
Za mu so jin ko an fuskanci ƙalubale a tafiyar?
Sosai kuwa, duk wani abu me kyau dama sai an fuskanci ƙalubale don haka wani abun ba ya bani mamaki idan yazo min musamman ma nasan wannan wani abu ne sabo da na zo da shi wanda mutane ba su tsammace shi ba, wasu kuma ba su taɓa tunanin samuwar sa ba, shi ya sa ma idan naje wa wasu da wannan batu sai jikin su ya mutu kuma su kashe min gwiwa da samin tunanin na zo da wani abu me wahala wanda bazai taɓa yiwuwa ba, din haka na sake tunani, wasu kuma su gayamin zai yiwu, amma zan sha wahala, wasu kuma sukan faɗa min gaka matashi baka san wasu ba Ina ma ace kai wani babba ne da ka kai matakin ‘professor’ da shi kenan kakar ka ta yanke saƙa, da irin waɗannan maganganu dai da dama wanda dukkannin su ban kalle su ba ballantana su yi tasiri akaina, abin da nake sawa arai komai ki ka ga ya tabbata to Allah ya yarda da wannan abun shi ya sa zai tabbata, sannan kuma wannan aikin ba na sakawa arai na cewa, nawa ne ni kaɗai Ina hakiƙance cewa, na al’umma ne musamman al’ummar Hausa, Ina faɗa wa al’umma cewa, ni iya aikina samar da wannan aiki sai kuma koyar da shi ga al’umma har mu samu ƙwararrun malamai a fannin, wanda hakan zai sa cikin ƙanƙanin lokaci mu samu zaƙaƙuran hausawa da za su iya wannan rubutu da karatu wanda hakan zai ba wa al’ummar damar yin amfani da wannan rubutun ta fanni daban-daban musamman harkar rubuce-rubuce da kuma ba da ilimi musamman idan Allah ya karɓi al’amarin, al’umma kuma suka maida hankali wajen ganin tabbatuwar sun yaɗa wannan rubutu aduniya ta hanyar yaɗawa.
Wani ƙalubale da na fuskanta ko nake fuskanta akwai matsala da nake samu wajen koyar wa wasu za su ce, wannan ai wahala ne idan na koya me zai amfanar min kuma menene ribata, wasu kuma su ce ai banda abun yi shi ya sa, wasu kuma suna ɗauka ta kamar ban san abin da nake yi ba, sai dai ahankali na fara shawo kan mutane har suka fara shiga aji wanda yanzu haka Ina da ɗalibai da dama, kuma Ina musu uzuri saboda nasan na zo wa al’umma da wani sabon abu da ba su san shi ba; don haka sai na sa wa kaina haƙuri da karɓar kowacce jarrabawar da zan fuskanta daga al’umma don akwai waɗanda na taɓa gayyata kawai suka ƙyalƙyale min da dariya, amma hakan bai sa na janye daga abin da nake yi ba. Sai kuma ƙalubale ɓangaren kuɗi da yake aiki ne babba ba ƙarami ba, yana buƙatar kuɗi masu yawa wajen gudanar da shi da kuma tabbatuwar sa, amma Ina iya nawa ƙoƙarin wajen yin duk abin da ya dace wajen kashe kuɗi idan buƙatar hakan ta taso, da yake ni ɗan kasuwa ne, Ina amfani ne da abun da nake samu a harkar kasuwa idan wani abu ya taso, amma duk da haka muna buƙatar wadatattun kuɗaɗe domin ganin tabbatuwar al’amarin.
Zuwa yanzu ko kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu a wannan aiki?
Eh, alhamdu lillahi. Mun fara samun biyan buƙata musamman ganin yadda al’umma suke ba mu goyon baya, kuma suke ƙaunar abinn tare da buƙatar waɗannan sababbin baƙaƙe, kuma a yanzu shirye-shirye sun yi nisa wajen samar da ‘pont mechanization’ na su waɗannan baƙaƙe wanda a yanzu haka su ne muka fi sa wa a gaba don ganin mun samar da su don amfanin al’umma da kuma ɗalibai, domin wannan ita ce hanya ɗaya da za mu samu damar amfani da waɗannan baƙaƙe ta hanyar rubutu da su a kwamfuta kuma mu saka su a manhajar kafafe daban-daban, domin amfani da rubutun, duniya ta zama komai sai ka tafi da zamani musamman a harkar ilimi, shi ya sa muka yi ƙoƙari ganin mun fara shirya darasi a kafafen sada zumunta kamar YouTube da sauran su, kuma muna fatan al’umma za su ba da haɗin kai wajen bibiyar abun da akeyi domin su zama ƙwararru su ma ta wannan fannin musamman idan har suka yarda za su iya.
Mun gode.
Ni ma na gode ƙwarai.

