Alƙalin Babbar Kotun Tarayya zai amsa gayyatar Kotun ɗa’ar Ma’aikata

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Babban Alƙalin Babban Kotun Tarayya, Mai Shari’a John Tsoho, ya mayar da martani ga gayyatar da ya samu daga Hukumar Kula da ƙa’idojin ɗa’a ga Ma’aikatan Gwamnati (CCB) dangane da batun cike takardar bayyana kadarori, yana mai sake jaddada ƙudirinsa na bin gaskiya da mutunta doka a dukkan matakai.

Wannan bayani na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da Daraktar Yaɗa Labarai ta Babbar Kotun Tarayya, Dakta Catherine Oby Christopher, ta aikewa da manema labarai, mai taken: “Dangane da gabatarwar Babban Alƙalin da kuma ranar da aka tsara domin bayyanarsa a gaban CCB.”

Kotun ta bayyana cewa Mai Shari’a Tsoho yana da cikakken niyyar ba da haɗin kai ga CCB kan gayyatar da aka yi masa. Wannan na zuwa ne bayan wani rahoto da Premium Times ta wallafa, inda ta ambato majiyoyi a cikin CCB da ke cewa an gayyaci Babban Alƙalin domin ya amsa tambayoyi kan wasu asusun banki da ake zargin bai bayyana su ba a cikin takardar kadarorinsa.

A cewar sanarwar, bisa haƙƙin da kundin tsarin mulki ya ba shi na tuntuɓar lauya da ya zaɓa, wakilinsa na shari’a, Cif Kanu Godwin Agabi, CON, SAN, ya nuna shirinsa na raka Mai Shari’a Tsoho zuwa gaban CCB da zarar ya dawo Nijeriya, kasancewar a halin yanzu yana waje domin dalilan rashin lafiya.

Kotun ta ce, an sanar da CCB wannan matsayi, tare da tabbatar da cewa Babban Alƙalin a shirye yake ya bayyana a gaban hukumar domin amsa dukkan tambayoyi cikin bin ƙa’idojin doka da kariyar kundin tsarin mulki. Domin sauƙaƙa tsara lokaci, an shaida wa CCB cewa duk wata rana a cikin makon da zai fara daga Litinin, 16 ga Maris, 2026, ta dace ga Mai Shari’a da lauyansa.

A cikin sanarwar, Mai Shari’a Tsoho ya sake jaddada ƙudirinsa na bin doka, gaskiya da kuma mutunta tsarin shari’a.

Rahoton Premium Times ya ce binciken da ta gudanar ya nuna zargin cewa Babban Alƙalin bai bayyana wasu asusu uku na bankuna ba. CCB kuwa ita ce hukuma ta tarayya da ke kula da batutuwan rikicin anfani da mukami da kuma cin zarafin ofis ga jami’an gwamnati.

Lamarin na faruwa kusan shekaru biyu bayan Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta sallami tare da wanke tsohon Babban Alƙalin Nijeriya, Walter Onnoghen, daga hukuncin da CCT ta yanke masa a 2019 kan zargin rashin bayyana kadarori. 

Kwamitin alƙalai uku ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Abba Bello Mohammed ne ya yanke hukuncin, inda ya umarci a buɗe dukkan asusun bankunan da aka rufe masa, bisa yarjejeniyar sulhu da aka cimma tsakanin lauyoyinsa da Ofishin Babban Lauyan Tarayya.

Kotun ɗaukaka ƙara ta kuma jaddada cewa CCT ba ta da hurumin gurfanar da wani jami’in shari’a kai tsaye ba tare da miƙa batun ga Majalisar Shari’a (NJC) ba, wadda ita ce ƙoli a ɓangaren kula da harkokin shari’a a ƙasar.

An rantsar da Mai Shari’a John Tsoho a matsayin alƙalin Babbar Kotun Tarayya a ranar 12 ga Nuwamba, 1998, sannan aka naɗa shi Babban Alƙalin kotun a ranar 13 ga Disamba, 2019. A halin yanzu shi ma mamba ne a cikin NJC.

Zargin da aka wallafa a kansa shi ne na baya-bayan nan da ya shafi wani babban jami’in shari’a da ke jagorantar ɗaya daga cikin kotuna mafi cunkoso a Afirka. Sai dai kamar yadda ƙa’idar doka ta tanada, zargi zargi ne kawai har sai an tabbatar da shi a gaban hukuma mai hurumi.

By ukarofi