Dimukraɗiyya: Gwamnan Sakkwato ya gana da shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu, ya gudanar da wani muhimmin taro da shugabannin ƙananan hukumomi 23 na jihar, mataimakansu da kuma kansiloli 244 domin tattauna hanyoyin da za a ƙara inganta dimokuraɗiyya a matakin ƙasa-ƙasa.

Taron, wanda ya gudana a Sakkwato, ya mayar da hankali kan muhimmancin al’ummomin karkara da unguwanni a tsarin siyasa, inda gwamnan ya bayyana cewa su ne ginshiƙin nasarar kowace gwamnati mai kishin jama’a.

A cewarsa, al’ummar ƙasa-ƙasa su ne mafi rinjayen masu kaɗa ƙuri’a kuma jigon magoya bayan gwamnati, don haka wajibi ne a riƙa tafiya da su a kowane mataki na tafiyar dimokuraɗiyya.

“Al’ummar ƙasa-ƙasa su ne ƙashin bayan tsarin siyasa, kuma ba za a taɓa wulaƙanta rawar da suke takawa ba,” inji gwamnan, yana mai jaddada cewa dimokuraɗiyya ba ta cika sai idan jama’a sun amfana da ribarta kai tsaye a muhallansu.

Gwamna Aliyu ya kuma yi bayanin cewa gwamnatinsa na aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa a sassa daban-daban na jihar, tare da kira ga shugabannin ƙananan hukumomi da su ɗauki irin waɗannan matakai a yankunansu domin kusantar da ci gaba ga jama’a.

A cewarsa, taron ya kuma yi nazari kan yadda aikin rajistar ‘ya’yan jam’iyya ta hanyar na’ura ke gudana a matakin ƙasa-ƙasa, domin gano ƙalubale da samar da mafita mai ɗorewa. Ya yaba da yadda magoya bayan APC suka fito kwansu da ƙwarƙwata wajen yin rajistar, tare da kira ga waɗanda ba su yi ba da su gaggauta cikawa.

Haka kuma, gwamnan ya bayyana cewa an yi bitar ƙarfi da raunin jam’iyyar APC a dukkan ƙananan hukumomi 23 na jihar, domin ɗaukar matakan da suka dace a inda ake buƙata, da nufin ƙara danƙon zumunci da ƙarfin jam’iyya a faɗin jihar.

A nasa jawabin, Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Sakkwato, Isa Saddiƙ Achida, ya yaba da salon shugabancin Gwamna Aliyu, yana mai cewa gwamnan na buɗe ƙofarsa ga jama’a da ’ya’yan jam’iyya a kowane lokaci, lamarin da ke ƙara ƙarfafa haɗin kai da amincewa tsakanin gwamnati da al’umma.

By ukarofi