TCN ya katse lantarki domin sabunta babban layin 330kɓ na Benin–Ajaokuta

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Nijeriya (TCN), reshen yankin Benin, ya sanar da jama’a cewa za a yi katsewar wutar lantarki na wucin-gadi a layin isar da wuta mai ƙarfin 330kɓ na Benin–Ajaokuta, domin bai wa aikin sake jera wayoyin wutar damar gudana a tashar Turn-In/Turn-Out da ke cibiyar samar da wutar Ihoɓbor.

Sanarwar na ƙunshe ne cikin wata takarda da Babbar Manajar Harkokin Hulɗa da Jama’a ta kamfanin, Ndidi Mbah, ta fitar. Ta bayyana cewa aikin ya fara ne a ranar Juma’a, 27 ga Fabrairu 2026, kuma zai ci gaba har zuwa Talata, 31 ga Maris 2026, daga ƙarfe 8:00 na safe zuwa 6:00 na yamma a kowace rana.

A cewarta, wannan aiki ya zama dole domin bai wa kwangilar TCN damar ci gaba da sabunta layin 330kɓ da ke haɗe da cibiyar samar da wutar Ihoɓbor. Ta aara da cewa layin na ƙetare manyan tituna a yankin Benin–Ajaokuta, lamarin da ya sa dole a riƙa katse wuta na wucin-gadi domin kare lafiyar jama’a.

Hukumomin kula da zirga-zirga da tsaro sun samu sanarwa, kuma za su kasance a shirye domin tabbatar da tsaron jama’a yayin gudanar da aikin.

Kamfanin rarraba wutar lantarki na Benin (BEDC), ba zai iya samar da wuta ga abokan huldarsa da ke yankunan UNIBEN, Oluku, Egba da Ihoɓbor ba na tsawon sa’o’i har goma a kowace rana a lokacin da aikin ke gudana.

Sai dai an bayyana cewa za a dakatar da aikin a kowace rana da ƙarfe 6:00 na yamma, bayan haka kuma za a maido da wuta ga layukan da abin ya shafa. Wannan na nufin BEDC za ta riƙa daukar wuta daga ƙarfe 6:00 na yamma zuwa 8:00 na safe a washegari domin waɗannan yankuna.

TCN ta nemi afuwar jama’a bisa duk wata takura da hakan zai iya haifarwa, tare da ba da tabbacin cewa za a maido da cikakken isar da wutar lantarki ga kamfanin rarraba wuta bayan kammala aikin.

By ukarofi