Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Majalisar Kula da Harkokin ’Yan Sanda ta ƙasa ta amince da naɗa Olatunji Disu a matsayin cikakken Sufeto Janar na Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa za a miƙa sunansa ga Majalisar Dattawa domin tantancewa da tabbatar da naɗin, kamar yadda tsarin mulki ya tanada.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ne ya fara naɗa Disu a matsayin mukaddashin Sufeto Janar a ranar 25 ga Fabrairu, 2026, bayan murabus ɗin tsohon Sufeto Janar, Kayode Egbetokun.
A wancan lokaci, mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa za a kira zaman Majalisar Kula da ’Yan Sanda domin duba naɗin, kafin a miƙa sunan ga Majalisar Dattawa domin amincewa ta ƙarshe.
Disu, mai shekaru 59, ya karɓi ragamar jagorancin rundunar a wani gajeren biki da aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke Louis Edet House a Abuja, jim kaɗan bayan da shugaban kasa ya yi masa ado da mukamin muƙaddashin Sufeto Janar.
Kafin wannan matsayi, Disu ya kasance Mataimakin Sufeto Janar mai kula da Sashen Binciken Manyan Laifuka na Rundunar (FCID Annex) da ke Alagbon, Legas. An ɗaga shi zuwa muƙamin Mataimakin Sufeto Janar ne a bara. A baya kuma, ya taɓa riƙe muƙamin Kwamishinan ’Yan Sanda a Jihar Ribas, sannan daga bisani aka mayar da shi Abuja a matsayin Kwamishinan ’Yan Sanda na Babban Birnin Tarayya.
