Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Kula da Jiragen ƙasa ta Nijeriya (NRC), ta sanar da ƙara yawan zirga-zirgar jiragen ƙasa a layin dogo na Abuja–Kaduna, sakamakon ƙaruwar fasinjoji da ke amfani da hanyar a kullum.
A cikin wata sanarwa da Babban Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Callistus Unyimadu, ya aikewa manema labarai, NRC ta ce sabon jadawalin tafiya zai fara aiki daga ranar 6 ga Maris.
Hukumar ta bayyana cewa ƙarin tafiye-tafiyen na da nufin samar wa matafiya zaɓuɓɓukan tafiya masu yawa, ƙara sassauci a harkokin aiki, da kuma inganta sabis a ɗaya daga cikin manyan layukan jirgin ƙasa mafi cunkoso a ƙasar nan.
Sanarwar ta tunatar da cewa layin ya fuskanci tsaiko a baya bayan harin bam na ranar 28 ga Maris, 2022, da kuma hatsarin fitar jirgi daga layi a ranar 26 ga Agusta, 2025.
Wazannan lamurra sun rage yawan jiragen da ke aiki daga uku zuwa guda ɗaya, tare da ƙaƙaba takunkumin gudu na wucin-gadi domin tsaro, da kuma rage yawan tafiye-tafiyen yau da kullum.
Sai dai hukumar ta ce yanzu an dawo da daidaito a harkokin aiki, kuma sakamakon ci gaba da buƙatar da fasinjoji ke nunawa, an yanke shawarar fazada sabis ɗin domin dacewa da tsammanin jama’a, baya ga sassauta wasu daga cikin takunkumin gudun wucin-gadi da aka sanya a baya.
Dangane da sabon jadawalin, za a riƙa gudanar da tafiye-tafiye uku a ranakun Juma’a, Lahadi, Asabar da Litinin tsakanin tashoshin Idu da Rigasa, yayin da za a yi sau biyu a ranakun Talata da Alhamis. A ranakun Talata da Alhamis, jirgin Idu–Rigasa zai tashi daga Idu da misalin ƙarfe 8:45 na safe, ya dawo daga Rigasa da ƙarfe 2:30 na rana.
A ranakun Juma’a da Lahadi kuwa, jiragen za su tashi daga Idu da ƙarfe 7:45 na safe da 3:15 na yamma, yayin da daga Rigasa za su tashi da ƙarfe 11:30 na safe. A ranakun Asabar da Litinin, jiragen za su tashi daga Rigasa da ƙarfe 7:15 na safe da 3:00 na yamma, sannan daga Idu da ƙarfe 11:00 na safe. Dukkan jiragen za su tsaya a tashar Kubwa kamar yadda aka tsara.
Hukumar ta shawarci matafiya su kula da sabon jadawalin tare da tsara tafiyarsu bisa ga sauyin da aka yi. Ta kuma sake jaddada aniyarta ta ci gaba da inganta ƙarfin aiki, amincin zirga-zirga, tsaro da kuma jin daɗin fasinjoji a dukkanin hanyoyin jiragen ƙasa na ƙasar.
