Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Kwamishinonin sun haɗa da Sani Ali Ahmed Daura wanda tsohon shugaban jam’iyar APC a jihar sai Hon. Mannir Ayuba Sulluɓawa.
An gudanar da bikin rantsarwar ne a zauren taron da ke a fadar Gwamnatin Jihar bayan Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta tantance su tare da amincewa da naɗin nasu.
A jawabin sa jim kaɗan bayan rasuwar,Gwamna Raɗɗa ya bayyana wannan mataki a matsayin wani muhimmin ci gaba wajen ƙarfafa tsarin mulki da kuma inganta aiwatar da manufofin gwamnatinsa.
Ya yaba da gudunmawar Hon. Sani Ali Ahmed wajen bunƙasa Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Katsina, inda ya bayyana rawar da ya taka tun daga lokacin da aka kafa jam’iyyar a matsayin sakataren farko, sannan daga baya ya zama shugaban jam’iyyar na jiha, lokacin da jam’iyyar ta samu manyan nasarori a zaɓuka, musamman a kakar zaɓe ta 2023.
Haka kuma, Gwamna Raɗɗa ya yabawa Hon. Mannir Ayuba Sulluɓawa, inda ya bayyana shi a matsayin gogaggen ma’aikacin gwamnati wanda ya yi aiki tuƙuru a ɓangarori daban-daban na aikin gwamnati, yana mai bayyana ƙwarin gwiwarsa cewa ƙwarewarsa za ta taimaka wajen ƙara inganta tafiyar da gwamnati da kyautata hidimar jama’a.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa ɗaya daga cikin naɗin na da nufin gyara rashin daidaito a wakilci, inda ya nuna cewa tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999, cikin birni a garin Katsina ba ta samu wakilci a matsayin Kwamishina ba.
Ya buƙaci sabbin kwamishinonin da su gudanar da ayyukansu da gaskiya, aminci da jajircewa, tare da yin aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran mambobin Majalisar Zartarwa domin tallafawa manufofin gwamnatinsa musamman a fannoni kamar tsaro, ilimi, lafiya, noma da bunƙasar tattalin arziki.
Bikin rantsarwar ya samu halartar mataimakin gwamna, Hon. Faruk Lawal, shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, Hon. Abdulkadir Mamman Nasir, shugaban ma’aikatan gwamnatin jiha, Alhaji Falalu Bawale, mambobin majalisar zartarwa ta jiha, manyan jami’an gwamnati, ‘yan siyasa, iyalan waɗanda aka rantsar, da sauran masu fatan alheri
