Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Babbar kotun tarayya da ke Abuja ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a James Omotosho ta wanke tare da sallamar dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Abba Kyari da ’yan uwansa, Mohammed Kyari da Ali Kyari, daga tuhume-tuhume guda 23 na zargin ƙin bayyana kadarori kamar yadda gidan talabijin na TVC ya rawaito.
Hukumar NDLEA ce ta shigar da ƙarar, inda ta tuhumi Kyari tare da ‘yan uwan nasa biyu da zargin rantsuwar ƙarya, domin ɓoye asalin wasu kadarori.
Sai dai a hukuncin da kotun ta yanke, ta ce NDLEA ta gaza gabatar da hujjoji masu ƙarfi da za su tabbatar da zargin, musamman kan mallakar filaye da ake cewa suna da alaƙa da Kyari.
Kotun ta kuma bayyana cewa masu gabatar da ƙara ba su kawo takardun da ke nuna cewa kadarorin da ke Fountain Estate, Kasana mallakin Kyari ba ne, haka kuma ba a gabatar da hujjojin da ke danganta shi da wasu kadarori a Asokoro, Abuja da kuma Maiduguri a Jihar Borno ba.
A bayanin kariyarsa, Kyari ya ce kadarorin da ke Borno mallakin mahaifinsa ne wanda ya gada tare da ‘yan’uwansa, kuma masu gabatar da ƙara ba su iya ƙaryata wannan ba.
Saboda haka, kotun ta yanke hukuncin sallamar su bakiɗaya daga zargin.
