Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
Aƙalla manoma 34 daga garin Maje da ke ƙaramar hukumar Taura da kuma wasu manoma daga ƙaramar hukumar Ringim a Jihar Jigawa sun amfana da injinan banruwa na zamani masu amfani da hasken rana, wanda Hukumar Kula da Kogunan Hadeja–Jama’are (HJRBDA) ta raba musu domin bunƙasa harkar noma.
Da yake jawabi yayin kaddamar da rabon injinan, Manajan Daraktan Hukumar, Injiniya Rabiu Suleiman Bichi, ya bayyana cewa an samar da tallafin ne a ƙarƙashin shirin gwamnatin tarayya na bunƙasa harkar noma a ƙasar nan.
Bichi ya ce shirin na daga cikin manufofin gwamnatin Shugaban ƙasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na tallafa wa manoma da kuma rage matsalolin da suke fuskanta, musamman tsadar man fetur da ake amfani da shi wajen banruwa.
Ya ƙara da cewa amfani da injinan banruwa masu aiki da hasken rana zai taimaka wajen sauƙaƙa wa manoma wahalhalu da kuma ƙara yawan amfanin gona, musamman a noman rani.
A cewarsa, shirin zai ci gaba da gudana domin ƙara bunƙasa noman rani da na damina a faɗin ƙasar nan, ta yadda Najeriya za ta samu wadataccen abinci har ma ta rika fitar da shi zuwa ƙasashen waje.
Bichi ya kuma yi kira ga manoman da suka amfana da injinan da su yi amfani da su yadda ya dace domin cimma burin da gwamnati ke da shi na inganta harkar noma.
A nasa jawabin, Mal. Mukhtar Aliyu Maje, wakilin Dagacin garin Maje, ya bayyana cewa injinan za su taimaka matuƙa wajen inganta aikin noma a yankin.
Ya ce manoman yankin sun daɗe suna fama da matsaloli da suka haɗa da lalacewar rijiyoyi da kuma tsadar man fetur da ake amfani da shi wajen aikin banruwa.
Mukhtar Aliyu ya nuna godiya ga hukumar Hadeja–Jama’are bisa wannan tallafi, tare da tabbatar da cewa manoman za su yi amfani da injinan yadda ya kamata domin bunƙasa noma.
A wani cigaban kuma, Manajan Daraktan Hukumar Hadeja–Jama’are, Injiniya Rabiu Suleiman Bichi, ya karɓi baƙuncin Manajan Daraktan Hukumar Kula da Gidan Ajiyar Namun Daji ta Jihar Kano, Hon. Musayyib Kawu Ungogo, a ofishinsa.
Da yake bayani kan makasudin ziyarar, Hon. Musayyib Kawu Ungogo ya ce sun ziyarci hukumar ne domin ƙulla dangantakar aiki tsakanin hukumomin biyu, musamman a fannin samar da ruwa ga dabbobin da ake kiyayewa a gidan ajiyar namun daji.
Ya ce ruwa na da matuƙar muhimmanci ga rayuwar dabbobi da kuma kiyaye muhalli, don haka suna fatan samun haɗin kai daga hukumar Hadeja–Jama’are wajen samar da ruwa mai inganci.
Ungogo ya kuma nuna jin daɗinsa bisa irin kyakkyawar tarbar da aka yi musu, tare da fatan cewa haɗin gwiwar zai taimaka wajen bunƙasa ayyukan da hukumomin biyu ke yi.
A nasa ɓangaren, Injiniya Bichi ya bayyana farin cikinsa da ziyarar, yana mai cewa wannan ita ce karo na farko da wata hukuma mallakar Jihar Kano ta kai irin wannan ziyara domin ƙulla alaƙar aiki.
Ya jaddada cewa samar da ruwa na daga cikin manyan ayyukan hukumar Hadeja–Jama’are, don haka za su yi iya ƙoƙarinsu wajen tallafa wa gidan ajiyar namun daji.
Bichi ya kuma tunatar da muhimmancin gidan ajiyar namun daji na Kano, wanda tsohon gwamnan jihar Alhaji Audu Bako ya kafa domin kiyaye dabbobin daji da kuma ilmantar da al’umma game da su.
Ya ce a yau mutane da dama ba za su iya ganin wasu daga cikin irin waɗannan dabbobi ba sai idan sun kai ziyara a irin waɗannan wurare.
