Kungiyoyin ‘yan kasuwa sun jajenta wa takwarorinsu na kasuwar Singa da ‘yan katako Rijiyar Lemo

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

Kungiyoyin ‘yan kasuwa a Jihar Kano sun jajanta wa takwarorinsu na Kasuwar Singa da Kasuwar ‘Yan Katako da ke Rijiyar Lemo bisa iftila’in gobara da ya tashi a kasuwannin a makwannin baya.

Gobarar dai ta yi sanadiyyar asarar dukiya mai yawa, tare da rasa rayuka da kuma jikkata wasu daga cikin al’umma.

Shugabannin kungiyoyin ‘yan kasuwar sun mika sakon ta’aziyyar ne a yayin wani rangadi da suka kai kasuwannin, inda suka bayyana al’amarin a matsayin wata jarrabawa daga Allah.

Sun yi addu’ar Allah ya mayar wa wadanda suka rasa dukiyoyinsu da mafificin alheri, tare da rokon Allah ya kare aukuwar irin wannan ibtila’i a nan gaba.

Kungiyoyin sun kuma yi kira ga ‘yan kasuwar da abin ya shafa da su kasance masu hakuri da juriya, tare da daukar lamarin a matsayin kaddarar Allah.

A cewarsu, Allah ne ke bayarwa kuma Shi ne ke karba, kuma yana iya ninka abin da aka rasa da mafi alheri a gaba.

Hakazalika sun yi addu’ar Allah ya gafarta wa wadanda suka rasa rayukansu, tare da rokon Allah ya bai wa wadanda ke jinya a asibitoci lafiya cikin gaggawa.

Daga cikin shugabannin kungiyoyin da suka mika sakon ta’aziyyar akwai Sakataren Kungiyar Masu Sayar da Lemon Fulebo, Alhaji Aminu Mai Gwal, da Alhaji Mustapha Shuaibu Sulaiman (Galadiman Market ‘Yan Manja), da Alhaji Bala Muhammad (Gidan Bala Koki ‘Yan Lemon Roba).

Sauran sun hada da Rabiu Usman Dankoli, wakilin SIMDA Zone 5, da Alhaji Safiyanu Abdullahi CK, Shugaban Kasuwar Kayan Marmari ta Na’ibawa ‘Yan Lemo.

Haka kuma akwai Mataimakin Shugaban Kasuwar ‘Yan Tumatir ta Kwanar Gafan, Salisu Ibrahim Kura, da Shugaban Kasuwar ‘Yan Katako ta Na’ibawa, Alhaji Salisu Mai Dukiya, ta hannun jami’in hulda da jama’a na kungiyar Abdulhadi Abdullahi.

‘Yan kasuwar sun kuma yi kira ga gwamnati da ta gaggauta amfani da tallafin da aka samu wajen gyara wuraren sana’ar ‘yan kasuwar domin su samu damar komawa kasuwancinsu.

Sun ce hakan na da muhimmanci matuka duba da irin halin da ‘yan kasuwar suka shiga sakamakon wannan gobara.

Haka kuma sun yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa gaggauta kafa kwamiti domin tsara yadda za a raba tallafin ga wadanda abin ya shafa, karkashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Faruk Ibrahim.

Kungiyoyin sun bayyana fatan cewa tallafin da gwamnati ke shirin bayarwa zai isa hannun wadanda gobarar ta shafa domin rage musu radadin asarar da suka yi.

By ukarofi