Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta yi wa ma’aikata 130 karin girma zuwa matakai daban-daban a ƙoƙarinta na ƙarfafa gwiwar ma’aikatan gwamnati domin su ƙara jajircewa wajen gudanar da ayyukansu da kuma inganta hidimar jama’a.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kai da Hulɗa da Jama’a na Hukumar Jin Daɗin Ma’aikata ta Jihar Kano, Jamilu Mustapha Yakasai, ya fitar a makon da ya gabata.
Sanarwar ta bayyana cewa an amince da karin girman ne bayan zaman tantance ma’aikata da hukumar ke gudanarwa a ƙarshen kowane wata, inda ake duba cancantar ma’aikata wajen samun karin girma, sauya wurin aiki da kuma daukar matakan ladabtarwa idan bukatar hakan ta taso.
Shugabar Hukumar, Hajiya Ladidi Ibrahim Garko, ta bayyana cewa daya daga cikin muhimman nauyin da ya rataya a wuyan hukumar shi ne sanya ido domin tabbatar da cewa ana bin dokoki da ka’idojin aikin gwamnati yadda ya kamata.
Ta kuma yi kira ga ma’aikatan gwamnati da su ƙara jajircewa wajen gudanar da ayyukansu domin ci gaban jihar da kuma samar da ingantaccen aiki ga al’umma.
Haka kuma Kwamishina na ɗaya a Hukumar, Alhaji Abdullahi Mahmud Umar, da Babban Sakataren Hukumar, Alhaji Sani Shehu Minjibir, sun jaddada muhimmancin aiki tukuru tare da bin dokoki da ka’idojin aikin gwamnati.
Sun bayyana hakan ne yayin zaman hukumar wanda ya samu halartar mambobi da daraktocin sassan hukumar, inda suka bukaci ma’aikata da su ci gaba da gudanar da aikinsu cikin gaskiya da riƙon amana.
