Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya bayyana cewa ajiyar kuɗaɗen waje ta Nijeriya – duka babba (gross) da kuma ta zahiri (net) – ta samu gagarumin bunƙasa a ƙarshen shekarar 2025, sakamakon ƙarfafa ginshiƙan ɓangaren waje da kuma ɗorewar gyare-gyaren manufofin tattalin arziki.
Cardoso ya ce, ajiyar kuɗaɗen waje ta zahiri ta tashi daga dala biliyan 3.99 a ƙarshen 2023 zuwa dala biliyan 34.80 a ƙarshen 2025, wanda ke nuna ƙaruwar kusan kashi 772 cikin ɗari. A cewarsa, wannan ci gaba ya samo asali ne daga haɓakar amincewar masu zuba jari, bayan aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki da suka jawo kwararar kuɗaɗen musayar waje zuwa ƙasar.
Ya bayyana hakan ne bayan taron kwamitin tsara manufofin kuɗi na CBN (MPC) a ranar 24 ga Fabrairu, 2026, inda ya ce jimillar ajiyar kuɗaɗen waje ta kai dala biliyan 50.45 zuwa ranar 16 ga Fabrairu, 2026. Haka kuma, ya ƙara da cewa ajiyar zahiri ta kai dala biliyan 34.80 a ƙarshen Disamba 2025.
A cewarsa, alƙaluman sun nuna ribar da aka samu daga ƙara gaskiya da sahihanci wajen tafiyar da kasuwar musayar kuɗaɗen waje. Wannan ya ƙara ƙarfafa amincewar masu zuba jari, ya jawo ƙarin kuɗaɗen waje, tare da inganta dabarun kula da ajiyar kuci domin kare jarin ƙasa, tabbatar da wadatar kuɗi da kuma ɗorewar tattalin arziƙi a dogon lokaci.
Gwamnan CBN ya jaddada cewa wannan bunƙasa ta nuna ƙarfafa katangar kariya ta tattalin arzikin waje cikin shekaru uku da suka gabata. Ya ce ajiyar zahiri ta 2025 kaɗai ta zarce jimillar ajiyar babba da aka samu a ƙarshen 2023, wadda ta tsaya a dala biliyan 33.22.
Haka kuma, ya bayyana cewa ajiyar zahiri ta tashi daga dala biliyan 23.11 a ƙarshen 2024 zuwa dala biliyan 34.80 a ƙarshen 2025, yayin da ajiyar babba ta ƙaru daga dala biliyan 40.19 zuwa dala biliyan 45.71 a wannan lokaci, wanda ke nuna karin dala biliyan 5.52. Wannan, a cewarsa, na nuna ƙara ƙarfin Nijeriya wajen cika alƙawuran waje, kare darajar naira da kuma tabbatar da juriya a fagen tattalin arziki.
Cardoso ya bayyana matsayin ajiyar ƙarshen 2025 a matsayin hujja mai ƙarfi da ke nuna tasirin sauye-sauyen manufofin CBN da gyare-gyaren ɓangaren waje. Ya kuma tabbatar da cewa bankin zai ci gaba da kula da kasuwar musayar kuɗi cikin tsari da ƙwarewa, domin tabbatar da daidaito, kwanciyar hankali da ɗorewar tattalin arzikin ƙasa, bisa dokokin da suka kafa shi.
