An gurfanar ɗan Chana a Nasarawa kan ha’inci

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, reshen Babban Birnin Tarayya Abuja, ta gurfanar da wani ɗan Chana mai suna Zhang Wen Hao a gaban Mai Shari’a Ibrahim Shekarau na Babbar Kotun da ke zaune a garin Mararabar Jihar Nasarawa.

Ana tuhumar Zhang ne da laifi guda da ya shafi ha’inci, kamar yadda takardar ƙarar ta bayyana.

A cewar ƙarar, Zhang a watan Maris na 2023 a yankin Suleja, ya yaudari wani mai suna Paul Yichol da N1,000 domin ya buɗe asusu a Bankin Access da sunansa da nufin amfani da shi wajen yin wasu haramtattun ayyuka.

Wannan aiki ya ci karo da sashe na 320 na dokokin arewacin Nijeriya, sannan akwai hukunci a kai a ƙarƙashin sashe na 322 na dokar.

Saidai, a yayin shari’ar, Zhang ya musanta wannan zargi da aka ɗora masa bayan da lauyan ɓangaren masu ƙara, Taiwo Aromolaran ya nemi kotun da ta sanya rana domin hukunci akan hujjojinsu, yana mai cewa sun shirya tsaf wajen gabatar da su a gare ta.

A yayin haka ne lauyan da ke kare Zhang, Michael Ukatu ya nemi kotun da ta bayar da belin abokin hulɗar nasa zuwa lokacin kammala shari’ar.

Bayan haka ne Alƙali Shekarau ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 12 ha Maris domin zama akan neman belin ɗan Chanan, inda kuma ya umarci ya cigaba da zama a hannun EFCC zuwa lokacin.

By Babaji