Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa Nijeriya ta samu gagarumin ci gaba wajen shirin gabatarwa da kuma ƙaddamar da sabon maganin rigakafin cutar ƙanjamau (HIV) mai suna Lenacapavir (LEN) a matsayin wata hanya ta Pre-Eɗposure Prophylaɗis (PrEP) domin ƙarfafa yaƙi da yaɗuwar cutar a faɗin ƙasa.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugabar Sashen Watsa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta Hukumar Yaƙi da Cutar ƙanjamau (NACA), Toyin Aderibigbe, ta fitar a Abuja.
A cewar sanarwar, Nijeriya na ƙara ƙaimi wajen shirye-shiryen shigar da rigakafin Lenacapavir, wani rigakafin HIV da ake yi wa mutum allura sau biyu a shekara, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin hanzarta daƙile yaɗuwar cutar.
Hukumar NACA ta bayyana cewa ana sa ran kayayyakin da ake buƙata domin fara shirin LEN PrEP za su iso ƙasar nan a cikin watan Maris, wanda hakan zai ba da damar fara aiwatar da shirin a matakai daban-daban.
Hukumar ta ce wannan mataki na daga cikin ƙudurin Gwamnatin Tarayya na ƙarfafa rigakafin HIV da kuma kusantar cimma burin daaile yaɗuwar cutar baki ɗaya.
Sanarwar ta ƙara da cewa, an kafa tsari na haɗin gwiwar ƙasa baki ɗaya domin tabbatar da cewa an ƙaddamar da shirin cikin ingantaccen tsari, tare da tabbatar da inganci da kulawa ta musamman a jihohin da aka bai wa fifiko.
Ta jaddada cewa Nijeriya na kan turbar da za ta kai ga fara aiwatar da LEN PrEP bisa matakai, tare da samun amincewar hukumomin da ke kula da magunguna, shirye-shiryen tsarin kiwon lafiya, horas da ma’aikata da kuma dabarun wayar da kan al’umma.
NACA ta bayyana cewa an riga an cimma wasu muhimman nasarori domin tallafawa fara shirin. Daga cikin su har da kammala nazarin yanayi da shirin ko jihohi sun shirya a jihohi goma da suka haɗa da Akwa Ibom, Anambra, Benuwe, Kuros Ribas, Ebonyi, Babban Birnin Tarayya Abuja, Gombe, Kano, Kwara da Legas.
Haka kuma, Hukumƙr Kula da Ingancin Abinci da Magunguna (NAFDAC) ta ba da amincewar doka ga maganin Lenacapavir, matakin da ya share fagen fara aiwatar da shirin a hukumance. Bugu da ƙari, an gudanar da horon kasa baki ɗaya ga masu horaswa a Abuja, sannan aka bi shi da horas da ma’aikatan lafiya a jihohin da aka zaɓo.
Hukumar ta kuma samar da kayayyakin Ilimantarwa, Wayar da Kai da Sadarwa (IEC) domin ƙara faɗakar da jama’a da kuma ƙarfafa karɓar wannan sabon zaɓin rigakafin HIV. NACA ta sake jaddada ƙudurin Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa hanyoyin rigakafi da kuma samar da sabbin dabaru na zamani domin rage sabbin kamuwa da cutar HIV a faɗin Nijeriya.
