Gwamnoni sun goyi bayan sabon tsarin tura kuɗaɗen mai kai tsaye

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyar Gwamnonin Jihohin Nijeriya (NGF), ta bayyana cikakken goyon bayanta ga sabbin gyare-gyaren da ke wajabta tura dukkan haƙƙoƙin kuɗaɗen shiga daga man fetur da iskar gas kai tsaye cikin Asusun Tarayya.

Kungiyar ta ce, wannan mataki yana da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da gaskiya a harkokin kuɗi, daidaito a tsari, da kuma bin tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulki.

Wannan matsayi na ƙungiyar na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Sadarwa na NGF, Yunusa Tanko Abdullahi, ya sanya wa hannu a ranar 2 ga Maris, 2026.

A cewar sanarwar, ƙungiyar ta yi nazari kan Umarni na Zartarwa na 9 da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaba wa hannu a ranar 13 ga Fabrairu, 2026, wanda ke da nufin daidaita hanyoyin shigar kuɗaɗen mai da iskar gas da tanade-tanaden kundin tsarin mulki, tare da fayyace iyakokin ayyukan hukumomin da ke kula da harkokin man fetur.

ƙungiyar ta bayyana cewa Umarni na Zartarwa na 9 ya tanadi cewa dukkan haƙƙoƙin gwamnati a ƙarƙashin yarjejeniyoyin rabon riba da makamantansu — ciki har da kuɗaɗen royalty oil, taɗ oil, profit oil da profit gas — za a riƙa tura su kai tsaye zuwa Asusun Tarayya.

Haka kuma, umarnin ya ƙara fito da sarari kan rabon ayyukan kulawa da sa ido a ɓangaren man fetur.

Shugaban NGF kuma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaƙ, ya jaddada cewa inganci da tabbataccen shigowar kuɗaɗen Asusun Tarayya su ne ginshiƙin tsarin rabon iko na kuɗi a Nijeriya.

Ya ce, “Asusun Tarayya shi ne aashin bayan tsarin kuɗaɗen da ke haɗa gwamnatocin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi.

Tsarin tura kuɗaɗen albarkatun ƙasa na ƙara ƙarfafa zaman lafiyar tattalin arziki a kowane mataki. Idan ana iya hasashen kuɗi, ana iya tsara ayyuka; idan an tsara, ana iya aiwatar da su yadda ya kamata.”

NGF ta kuma lura cewa kuɗaɗen mai da iskar gas na ci gaba da kasancewa muhimmin ɓangare na kuɗaɗen shiga da ake rabawa a ƙasa, wanda ke tasiri kai tsaye kan shirye-shiryen manyan ayyuka, ɗorewar bashi, gina ababen more rayuwa da kuma samar da ayyukan jinƙai ga jama’a a matakan tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi.

ƙungiyar ta yi nuni da sanarwar da Kwamitin Raba Kuɗaɗen Asusun Tarayya (FAAC), ke fitarwa a baya-bayan nan, inda aka samu bambance-bambance tsakanin jimillar kuɗaɗen da aka tara da kuma adadin da aka raba a ƙarshe. A cewar NGF, abin da ake rabawa ne a ƙarshe ke ƙayyade ikon kuɗin jihohi wajen aiwatar da ayyukansu.

Gwamnonin sun yi gargaɗin cewa duk lokacin da tsarin tura kuɗaɗe ya rikice ko ya zama mai wahalar fahimta, hakan na rage tabbas a hasashen kuɗi, lamarin da ke kawo cikas ga tsara manyan ayyuka a dukkan matakan gwamnati. Sun jaddada cewa yayin da yawan al’ummar Nijeriya ya haura miliyan 220, jihohi ne ke kan gaba wajen samar da ilimi, kiwon lafiya na matakin farko, ababen more rayuwa da kuma tsaro, don haka suna buƙatar tabbataccen tsarin shigowar kuɗaɗe domin sauke nauyin da ke kansu.

A ƙarshe, NGF ta sake nanata aniyarta ta yin aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin tarayya da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa waɗannan gyare-gyaren kuɗi sun haifar da ci gaba mai ma’ana ga ’yan Nijeriya.

By ukarofi