Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wata ’yar kasuwa ’yar Nijeriya ta fito fili a kafafen sada zumunta tana nuna mamaki da kaɗuwa bayan da ta ce jami’an Hukumar Haraji ta Nijeriya sun aike mata da takardar kimanta haraji da ya kai Naira miliyan 11.7.
A cikin wani bidiyo da ta wallafa, ’yar kasuwar ta bayyana cewa jami’an haraji sun ziyarci shagonta tare da lissafa mata bashin haraji tun daga shekarar 2022, alhali a cewarta a wancan lokacin ba ta fara amfani da sabon sunan kasuwancinta ba, haka kuma ba ta buɗe asusun kasuwanci a ƙarƙashin wannan suna ba.
Ta yi tambaya kan yadda aka kai ga wannan adadi mai yawa, tana mai jaddada cewa harkokin kasuwancinta ba su fara gudana a shekarar da aka ambata ba. Ta kuma yi zargin cewa mai yiwuwa jami’an sun samo bayanan kasuwancinta ne daga shafinta na Instagram, ganin yadda aka rubuta suna da adireshin kasuwancin da kura-kurai.
A cewarta, idan aka yi cikakken bincike a kan bayanan asusun ajiyarta, za a gano cewa ba ta samu kuɗin shiga a lokacin da aka jingina mata bashin ba. Ta bayyana cewa sunan asusun kasuwancinta ma ba haka yake ba kamar yadda aka rubuta a takardar kimantawar, lamarin da ke ƙara jefa shakku kan sahihancin lissafin.
Bayan wannan lamari, ’yar kasuwar ta sanar da cewa daga yanzu za ta fara karɓar kaso 7.5 cikin ɗari na Harajin Kuɗin Kaya (VAT) a kan dukkan kayayyakin da take sayarwa, domin rage nauyin da ya hau kanta. Ta roƙi kwastomominta da su fahimci halin da take ciki, tana mai cewa ba ta da wani zaɓi face ta ɗauki wannan mataki.
Maganganunta sun jawo martani iri-iri daga jama’a a kafafen sada zumunta. Wasu sun ce gwamnati na da damar duba bayanan asusun banki domin tantance kuɗin shiga, yayin da wasu suka nuna damuwa cewa irin waɗannan matakai na iya kassara ƙananan ’yan kasuwa. Akwai kuma waɗanda suka ba ta shawarar ta je ofishin hukumar domin gabatar da dukkan takardunta don a sake duba lamarin.
Lamarin ya sake tayar da muhawara kan yadda ake aiwatar da tsarin haraji ga ƙananan da matsakaitan ’yan kasuwa, musamman a wannan lokaci da ake fama da matsin tattalin arziki.
