An yi kira ga Gwamnan Katsina ya shiga lamarin aikin hanyar Bakori zuwa Funtua

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban ƙungiyar cigaban yankin Funtua ya yi kira ga Gwamnan Katsina ya shiga lamarin aikin hanyar Bakori zuwa Funtua a hira da manema labarai a Katsina.

Ya ce kiran ya zama dole ganin yadda hanyar ta lalace da ta kai ana fashi da makami ga lalacewar ababen hawa.

Kwamred Suleiman ya bayyana cewa wannan hanya da ta tashi daga Funtua ta bi ta Bakori itace ta wuce Malumfashi zuwa gidan mutum ɗaya ta kai shekaru 40 da gina wa.

Ya ce banda ma fashi da makami da lalacewar ababen hawa akwai yawaitar hare haren ‘yan bindiga musamman a kan hanyar Funtua zuwa Bakori.

A kan haka Suleiman ya yi kira ba wai ga gwamna kaɗai, har da ‘yan majalisar ƙasa da manyan masu faɗa a ji a yankin da suyi duk abinda za su iya yi wajen ganin gwamnatin tarayya ta fara aikin hanyar kafin zuwan Damina.

Shugaban ƙungiyar ya yabawa Gwamna Dikko Raɗɗa bisa yadda ya gina tare da faɗaɗa hanyoyi na zamani a Funtua Katsina da Daura.

Ya ce gina titunan zai faɗaɗa kasuwanci da inganta tattalin arzikin jihar.

Ya jinjinawa Sanata Muntari Dandutse da Kwamishina Musa Adamu Funtua kan tallafi na kayan masarufi da suka sanarwa al’ummar yankin a cikin wannan wata mai alfarma.

Kwamred Suleiman ya ce mako guda ke nan ƙarƙashin ƙungiyar su suke ci da ciyar da masu ƙaramin ƙarfi da abincin buɗe baki a yankin.

By ukarofi