Sojojin Isra’ila 462 da jami’an Mossad 32 ne suka mutu a kwanakin ukun farko na yaƙin Iran da Isra’ila

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Hukumar leƙen asiri ta Rasha ta tabbatar da cewa Isra’ila ta rasa damar mallakar makamin nukiliya na Dimona, tare da asarar manyan masana kimiyyar nukiliya 11 a cikin kwanaki uku na farko bayan Iran ta mayar da martani.

Rahoton ya kuma bayyana cewa a cikin wannan lokaci Isra’ila ta yi asarar janar-janar na rundunar sojin ƙasar (IDF) guda 6, da jami’an sojin sama 198.

Kazalika, an ce sojoji 462 da kuma jami’an Mossad 32 sun mutu a cikin kwanaki uku na farkon mayar da martanin da Iran ta kai.

By ukarofi