Abuja: An halaka ɗan ta’adda yayin da dakarun tsaro suka ceto ‘yan Kubwa da aka sace

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Dakarun tsaro na ‘7 Guards Battalion’ na rundunar sojojin Nijeriya, sun yi nasarar ceto mutane 19 da aka yi garkuwa da su tare da halaka ɗan ta’adda a yayin wani atisaye da aka gudanar a Birnin Tarayya Abuja.

Mataimakin Daraktan hulɗa da jama’ar dakarun na riƙo, Laftanal Olawuyi Itunuoluwa ya bayyana haka a wata takarda, yau Asabar.

A cewarsa, an gudanar da atisayen ne a yankin Gidan Dogo da ke Ƙaramar Hukumar Bwari bayan samun wani bayani na sirri a game da mutanen da aka sace a Byazhin da ke Bwari.

Sojojin sun aiwatar da atisayen ne tare da haɗin-gwiwar jami’an rundunar ‘yan sanda da kuma ‘yan bijilante.

A lokacin atisayen, an yi ba-takashi tsakanin jami’an da ‘yan bindigar, inda a nan aka halaka guda daga cikinsu yayin da da dama suka tsere ɗauke da raunukan harbin bindiga, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Haka kuma dakarun sun ƙwato bindiga ƙirar AK-47 da wata ta gargajiya, tare da ceto baki ɗaya mutane sha taran ba tare da sun jikkata ba.

A halin yanzu, waɗanda aka ceton suna karɓar magani, yayin da sojojin suka mayar da sansanin atisayensu Bwari da cigaba da yin sintiri domin kare yankin daga ta’addanci.

By Babaji