Gwamnatin Nijeriya ta fitar da lambobin kiran gaggawa ga ‘yan Nijeriya a Gabas ta Tsakiya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta fitar da lambobin waya na kiran gaggawa ga ‘yan Nijeriya da ke zama a ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya sakamakon ƙaruwa da rikicin yankin ke yi, wanda ya janyo fargaba ga lafiyar ‘yan ƙasa.

Ma’aikatar Harkokin Waje ta bayyana haka a wata takarda domin taimaka wa ‘yan ƙasa su samu tuntuɓa cikin gaggawa idan buƙatar hakan ta taso.

Ga cikakken jerin lambobin gaggawa da gwamnatin ta bayar:

Iran: +989393216872, +989024165493

Israel: +972543340414, +972503673175

Jordan: +962795669949, +962799430414

Lebanon: +96181669403, +96170848080

Qatar: +97466802029, +97450733786

Saudi Arabia: +966503862894, +966532198524

United Arab Emirates: +971504252546, +971503761332

An kuma umurci ‘yan Nijeriya da su ajiye waɗannan lambobin a wayoyinsu na hannu kuma su riƙa shafar ofisoshin jakadanci da konsule da sun bukaci taimako na gaggawa.

Kazalika, an shawarce su da su bi duk shawarwarin tsaro na hukumomin ƙasashen da suke ciki domin kare lafiyarsu yayin da rikicin ke cigaba da ta’azzara.

By Babaji