Sufeto Janar Disu ya maye gurbin Hundeyin da Anthony Placid a matsayin kakakin ‘yan sanda

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sufeto Janar na ‘yan Sanda, Olatunji Disu, ya amince da naɗin Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda (DCP), Anthony Okon Placid a matsayin sabon kakakin rundunar.

Hakan na zuwa ne bayan cire ACP Benjamin Hundeyin daga muƙamin, a wani sauyi da aka yi a sashen hulɗa da jama’a na rundunar.

Rahotanni sun ce DCP Okon Placid ƙwararren jami’in ɗan sanda ne da ya taɓa aiki a fannoni daban-daban da suka haɗa da gudanarwa, ayyukan tsaro, leƙen asiri da kuma ayyukan wanzar da zaman lafiya na ƙasa-da-ƙasa.

A wata sanarwa da Hedikwatar rundunar ta fitar a yau Lahadi dak e ɗauke da sanyaye hannun ACP Hundeyin, hukumar ta ce Placid ya fara aiki a ƙarƙashinta ne tun a shekarar 1996 bayan kammala karatu a makarantar horar da ‘yan sanda da ke Wudil.

A baya-bayan nan ya riƙe muƙamin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar a Jihar Adamawa, sannan ya riƙe irin muƙamin a Kwalejin horar da ‘yan sanda da ke Jos a Jihar Filato.

By Babaji