‘Yan sanda sun fara tantance sababbin kuratan da za a ɗauka aiki

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar ‘Yan sanda a Jihar Jigawa, ta ce ta kammala shirye-shiryen fara tantance masu sha’awar shiga aikin kurtun ɗan sanda da suka fito daga jihar.

Kakakin rundunar yan sandan jihar SP Shiisu Lawan ya bayyana hakan, inda ya ce za a fara gudanar da tantancewar daga ranar 9 ga watan Maris har zuwa 18 ga Afrilu, 2026.

Ya shawsrci waɗanda abi nya shafa da su duba sahfin yanar gizo na ɗaukar aikin domin sanin matsayarsu, sannan su zo wajen aikin cikin da’a gami da cika duk ƙa’idojin da aka gindaya.

A cewarsa, za a gudanar da tantancewar ne a hedikwatar ‘yan sanda da ke Dutse, babban birnin jihar.

Kazalika, ya yi gargaɗin cewa dukkan wanda aka a uda laifin saɓa wa ƙa’idojin da aka bayyana, ba zai samu shiga sahun waɗanda za a tantance ba.

By Babaji