Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara ta yi maraba da Gwamna Dauda Lawal da magoya bayansa cikin jam’iyyar.
Wannan yana ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na jihar Yusuf Idris ya sanya wa hannu a yammacin yau.
Sanarwar ta bayyana cewa, shugabannin jam’iyyar, ciki har da ƙaramin ministan tsaro, Bello Muhammad Matawalle, sun bayyana ƙwarin gwiwar cewa shigar Lawal zai ƙarfafa zumunci tsakanin mutanen Zamfara da kuma ƙara wa jam’iyyar ƙwarin gwiwa a babban zaɓen 2027.
Jam’iyyar ta tabbatar wa Gwamna Lawal cikakken goyon baya da haɗin kai daga mambobin jam’iyyar, inda ta amince da shi da magoya bayansa a matsayin cikakkun ‘yan jam’iyya da suka cancanci dukkan gata.
Jam’iyyar tayi addu’ar cewa wannan ci gaban zai ɗaukaka haɗin kai da kuma bunƙasa “Ajandar Sabon Fata” ta Shugaba Bola Tinubu.
APC ta buƙaci ‘yan jam’iyyar da su goyi bayan wannan ci gaban, ta hanyar tabbatar da nasarar jam’iyyar da kuma ɗorewar tattalin arzikin Jihar ta Zamfara.
