Da Ɗumi-Ɗumi: An bada rahoton halaka Fraministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Litinin kafar yaɗa labarai ta Tasnim a ƙasar Iran ta yi zargin cewa akwai yiwuwar Fraministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya rasu ko ya jikkata a yayin da yaƙi tsakanin ƙasashen biyu ya yi ƙamari.

A wani rubutu da ta wallafa wanda ya karaɗe kafafen sadarwa, kafar ta yi ikirarin ne sakamakon rashin ganin sababbin hotuna ko bidiyonsa.

An gano cewa bidiyonsa na ƙarshe da aka wallafa a sahihin shafinsa ya kai kusan makonni uku, yayin da hotunan ƙarshe kuwa sun kai tsawon kwanaki huɗu.

Tun daga lokacin saidai a ga wasu rubuce-rubuce da ake danganta shi da su a kafafen watsa labarai ba tare da wasu sabbin hotuna ko bidiyo ba.

Haka kuma, an gano cewa yadda aka saba shi ne a ga ya bayyana a bidiyo aƙalla sau ɗaya ko guda uku a kullum. Rashin ganin fitar da ire-iren waɗannan biliyoyin na tsawon kwanaki ya jefa kokwanto da zargi akan ko yana raye.

Wasu majiyoyin kafafen labaran Isra’ila sun ruwaito cewa a ranar 8 ga Maris an ƙarfafa tsaro a gidan Netanyahu ciki har da ƙoƙarin bada kariya ga munanan hare-hare akan yankin nasa.

A cewar bincike, majiyoyi da ke kusa da tsare-tsaren harkokin wajen Isra’ila sun ce an soke wata ziyara da surikin Shugaba Donald Trump, Jared Kushner ya nufi kai wa Isra’ilan a gobe Laraba saboda barazanar hare-haren.

Saidai har yanzu ba a sanar da mutuwar fraministan ba a hukumance daga ɓangaren hukumomin Isra’ila ko magantuwa akan ikirarin rahoton, kamar yadda IntelRegion ta ruwaito.

By Babaji