Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
A ƙasa da mako guda mummunan rikici ya ɓarke a yankin Gabas Ta Tsakiya, tsakanin ƙasashen Amurka da Isra’ila a gefe guda da kuma ƙasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Rikici ne wanda an daɗe ana hasashen faruwarsa, sakamakon yadda dangantaka ta daɗe tana tsami tsakanin ƙasar Amurka da Iran, ganin yadda Amurka ke cigaba da goya wa ’yarlelenta, wato ƙasar Yahudawan Isra’ila baya tana cin karenta babu babbaka, kan raunanan ƙasar Falasɗinu da mujahidan ƙungiyar Hizbullahi na ƙasar Lebanon. Da ma yadda take yi wa dokokin ƙasa da ƙasa karan tsaye, wajen barazana ga sauran ƙasashen Larabawa da ke maƙwaftaka da ita.
Duk wani manazarci kan harkokin da ke gudana a yankin Gabas ta Tsakiya ya san irin cin kashin da Amurka take yi wa ƙasashen Larabawa, mamaye harkokin su na kasuwanci, da yi musu barazana kan siyasar su ta cikin gida, da sanya musu takunkumi kan harkokinsu na tsaro. Ta kai matakin da sai abin da Amurka da Isra’ila suke so haka za a yi a waɗannan ƙasashe, da shugabanninsu suka zama ’yan kore kuma karnukan farautar manyan azzaluman duniya.
Ƙasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ce kaɗai ta zama Zakka a wannan yankin, albarkacin Juyin Juya Halin Musulunci da ya auku a ƙasar fiye da shekaru 40, wanda ya sauya siyasar ƙasar, tattalin arziƙinta da cigabanta. Duk da ƙalubalen tsaro da ƙasar ta riƙa fuskanta a baya, sakamakon juyin juya hali da aka yi a ƙasar, daga ’yan tawayen Mujahidun Khalƙ, da Kallafaffen Yaƙin shekaru takwas da Amurka ta haddasa a tsakanin Iran da Iraƙi, lokacin tsohon hamɓararren shugaban ƙasar Saddam Hussain. ƙasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta gamu da matsaloli masu yawa waɗanda Amurka da Isra’ila ke angiza mata ta ƙarƙashin ƙasa, duk don ƙoƙarin ganin gwamnatin Musulunci ƙarƙashin jagorancin manyan malaman addini irinsu Ayatullahi Khumaini da magajinsa Shahidi Ayatullah Ali Khamenei, ba ta samu nasara ba, kuma ba ta cigaba da samun tasiri ba a duniya ba.
Karfin da Iran ke samu ta fuskar tsaro da ƙere-ƙeren makamai da kimiyya da fasaha da magunguna, ya sa waɗannan azzaluman duniya ke ganin barinta ta cigaba da wanzuwa babbar barazana ce ga muradunsu a Gabas ta Tsakiya. Yayin da su ma a nasu ɓangaren shugabannin Iran suka yi ta jaddadawa cewa ba za su sassautawa Amurka da Isra’ila ba, har sai sun sake wa Musulunci mara, kuma sun janye daga mamayar da suka yi wa ƙasar Falasɗinu da yakunan da ta mamaye na ƙasashen Musulmi, irin su Lebanon da Jordan. Sai dai duk da wannan gwagwarmaya da ƙasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran take yi don kare ’yanci da martabar addinin Musulunci, shugabannin ƙasashen Larabawa ba su ba ta haɗin kai da goyon bayan da take buƙata daga gare su ba. A maimakon haka ma, sai suka riƙa munafurtar ta, suna yi mata zagon ƙasa da taya Isra’ila da Amurka leƙen asiri, don a karya lagonta.
Waɗannan ƙasashe ciki har da ƙasar Saudi Arabiya da ake yi wa kallon alƙiblar al’ummar Musulmin duniya, sun riƙa bai wa Amurka da ‘yan kanzaginta dama suna kafa sansanoni da jibge makamai da jiragen yaƙi a wasu sassan ƙasashen su, domin zama barazana ga ƙasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran, da sunan ba su kariya da tsaro.
Yunƙurin ƙasar Iran na mallakar makamin Nukiliya ya zama babban abin damuwa ga Amurka da Isra’ila, ganin cewa matuƙar babbar abokiyar gabar su ta mallaki irin wannan makami, zai iya zama musu abu mawuyaci su iya kifar da ita, ko kuma samun galaba a kanta. Don haka suka riƙa sanya mata takunkumi iri-iri da matsin lamba, kan wannan cigaba da take samu ta fuskar ƙere-ƙeren makamai da nasarori da take cigaba da samu a ɓangaren kimiyya da fasaha. Hakan ya jefa ƙasar cikin wani matsanancin yanayi, da durƙushewar al’amura, musamman ta fuskar tattalin arziki, ta yadda rayuwar jama’ar ƙasar ta shiga halin ƙunci da talauci.
Lokaci da dama, Amurka da Isra’ila sun yi ta amfani da ’yan adawar siyasa da wasu baragurbin ‘yan ƙasar da suke yi wa azzaluman ƙasashen yamma leƙen asiri, wajen haddasa rigingimu na cikin gida, zanga-zangar ƙin jinin gwamnati saboda matsin rayuwa, da ma yunƙurin juyin mulki. Amma duk da haka, haƙar su ba ta cimma ruwa ba, dakarun juyin juya hali da sauran jami’an tsaro masu kishi sun cigaba da zama garkuwa ga tsarin Musulunci na ƙasar. Sannan kyakkyawan jagoranci daga manyan malaman addini na ƙasar ya taimaka wajen ƙarfafa haɗin kan ƙasar, da tsayuwarta akan manufar juyin juya halin da aka gina ƙasar akai, da kuma tasirin tarbiyyar aƙidar Musulunci da ƙasar take kai.
Duk da matsin lamba da ƙasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cigaba da fuskanta daga hukumomin ƙasa da ƙasa akan yunƙurin ta na mallakar makamin nukiliya, da haɗin kan da take bayarwa wajen bincike da sharuɗɗa da ake gindaya mata, hakan bai sa Amurka da Isra’ila sun saduda ba, har sai da suka tsokano ta da yaƙi bisa zargin tana taimakawa ƙungiyoyin ta’addanci irin su Hamas da Hizbullah, da makamai da kuɗaɗe, suna kai wa Isra’ila hare-hare.
Harin gwajin ƙwanji da Isra’ila ta kai wa Iran da martanin da ta mayar mata a tsakanin ranakun 13 zuwa 24 ga watan Yuni na shekarar 2025, wanda nan da nan aka yi gaggawar shiga tsakani, don ganin zafin naman da Iran ta nuna, ya sa Amurka da Isra’ila komawa kan teburi don auna yadda za su ɓullo mata, da nufin karya ƙarfinta, da lalata cibiyoyin nukiliyarta da makaman da take inganta su, don hana ta samun ƙarfin da zai taimaka ta iya samun galaba a kansu watarana.
Harin haɗin gwiwa da Amurka da Isra’ila suka kai wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran cikin wata mai tsarki na Ramadan, a ranar 28 ga watan Fabrairu, 2026 da kisan gillar da suka yi wa jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na ƙasar Ayatullah Ali Khamenei da wasu manyan kwamandojin yaƙin ƙasar, shi ya buɗe ƙofar faruwar wannan yaƙi da yanzu duniya take gani a matsayin masomin Yaƙin Duniya na Uku. Duk da kawo yanzu ana ganin ƙasar Iran ce kaɗai, da tallafin dakarun Houthi na ƙasar Yemen, da kuma gwarazan ƙungiyar Hizbullah, take yaƙi da manyan ƙasashen Amurka da Isra’ila, masu makamin nukiliya da ƙarfin soja, yayin da sauran ƙasashen Larabawa irin su Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Saudi Arabiya, ƙatar, Kuwait, Jordan, da Bahrain, suke mara wa ƙawancen Amurka da Isra’ila baya. Amma akwai hasashen idan wannan yaƙi ya cigaba, wasu manyan ƙasashen duniya za su bayyana matsayarsu, da shiga cikin yaƙin gadan-gadan. ƙasashe irin su Rasha da China, Afghanistan da Yamen tuni sun bayyana goyon bayan su ga ƙasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kodayake kawo yanzu ba su shiga cikin yaƙin kai-tsaye a zahiri ba.
Wasu rahotanni sun bayyana yadda jami’an tsaro a Tarayyar Daular Larabawa suka kama wasu jami’an leƙen asirin ƙasar Isra’ila na Mossad suna ƙoƙarin dasa bama-bamai a ofishin jakadancin Amurka a ƙasar, da nufin ƙara tunzura Amurka da sauran ƙasashen Larabawa su shiga yaƙin gadan-gadan. Kamar yadda aka jiyo shugabannin ƙasar Saudi Arabiya na shirin ɗaukar matakin soja kan Iran, bayan harin da ake zargin Iran ɗin ta kai ofishin jakadancin Amurka da ke Riyadh.
Harwayau, an jiyo Mataimakin Shugaban Majalisar Tsaron ƙasar Rasha kuma tsohon shugaban ƙasa Dmitry Medɓedeɓ, yana cewa, Yaƙin Duniya na Uku bai fara ba tukunna, amma zai iya ɓarkewa a kowane lokaci idan Trump ya ci gaba da tafiya a kan wannan salon nasa na yanzu. A cewarsa, ta hanyar yanke shawarar kai hari kan Iran, Trump ya jefa dukkan Amurkawa cikin mummunan haɗarin rasa rayuka.
Sai dai daga bayanan da ke fitowa daga Amurka da ƙawayenta, akwai alamun ba za ta bari yaƙin ya kai wancan matakin ba, duk da kalaman da aka rawaito Shugaban Amurka Donald Trump yana cewa yaƙin ba zai wuce makwanni shida ba. Sakamakon yadda tun daga yanzu Amurka da Isra’ila suka fahimci faɗan ya wuce yadda suke tunani da kuma shirin da suka yi masa tun da farko. Musamman ma yanzu da rahotannin da ba su inganta ba ke nuni da cewa Firaministan Isra’ila, Benjamin Natenyahu, ya rasa ransa a wani mummunan hari da Iran ta kai a birnin Tel Aɓiɓ, yayin da manyan jami’an sojan ƙasar Isra’ila ke gudanar da wani taron sirri.
Masana dai na ganin wannan yaƙi da ake yi wa laƙabi da Gurnanin Zaki, yana iya rincaɓewa ya haifar da mummunan al’amari a yankin Gabas ta Tsakiya, da ma tattalin arziƙin duniya bakiɗaya, idan har ba a shawo kan lamarin da wuri ba. Ko babu komai yanzu Amurka da Isra’ila sun gane Iran ba kanwar lasa ba ce, kamar yadda suka yi zato a baya. Sannan yadda Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta haukace kan kisan gillar da Isra’ila ta yi wa jagoran addini na ƙasar, ya tabbatar da cewa, Amurka da Isra’ila da ma sauran duniya bakiɗaya sun fahimci lallai kai wa Iran hari da aka yi tamkar an tsokano gidan rina ne!
