Daga ALI ABUBAKAR SADIK
Kusan duk abinda kasar Iran ta alƙawarta cewa za ta aiwatar matukar Amurka da Israila su ka kai mata hari, to a kwana na ukun wannan yaki babu Wanda ba ta aiwatar ba. Sun lashi takobi kaiwa duk kadarorin Amurka da ke Gabas ta tsakiya da Israila hari. Sannan za su rufe zirin mashigar Tekun Pasha, wato Straight of Hormuz. Zuwa yanzu sun kai hari a wurare 27 a kasashen Israila, Saudi Arabia, UAE, Kuwait, Bahrain, ƙatar, Jordan, Oman da sauransu.
Sakamakon kashe Ayatollah Ali Khamenei, mutane da dama sun dauka Iran zata maida martani cikin fushi ta hanyar antaya missiles dinta zuwa kasar Israila, kamar yadda aka gani a baya a yakin June 2025. A’a, yanzu da alamu su na bin zayyanannen tsarin yaki da su ka tsara. Kuma idan ka yi nazarin abinda su ka aiwatar, tabbas akwai hikima da amfani da kwakwalwa ba da zuciya ba wajen mayar da martani.
A awannin farko na maida martani, abu na farko da Iran ta hara shine waccan katafariyar cibiyar sansano makamai da wurwuri (Early warning Radar system) mai karfin da zai iya sansano an harba missile a da’irar kilomita 5000 daga inda wannan na’ura ta ke a girke a kasar ƙatar. Wannan na’ura, cikin minti shida zata iya sanar da duk wani jirgin yaki na sama da na ruwa da batira masu kakkabo makamai a duk fadin gabas ta tsakiya. Ba kawai sanarwa ne aikinta ba, zata iya tantance karfin gudu na makamin da Iran ta harbo, da inda ya nufa. Don haka wannan na’ura na iya sanar da daruruwan baturan THAAD da ke warwatse a sansanonin Amurka da Israila da jiragen ruwa a fadin gabas ta tsakiya.
Wannan Radar, tamkar ita ce zuciyar kariyar Gabas ta tsakiya daga hara-haren makamai masu linzami. An gina ta a kan tsabar kudi Dala biliyan $1.1. Cikin awannin farko na martanin Iran ta rugurguza ta. Illar ba ta tsaya a kan asarar wannan dimbin dukiya da aka kashe ba, mafi illa shine kasancewar makanta babbar kariyar da kasashen ke tunkaho da ita wajen kakkabo makamai masu linzami. A maimakon mintuna shida na shiryawa domin aikin da sauran makaman kakkabo makamai masu linzami ke da shi, rashin wannan na’ura ya maida lokacin minti guda kacal.
Abu na gaba da Iran ta yi shine amfani da tsoffin makamai marasa karfi sosai da drones wajen kai hare-hare a fadin gabas ta tsakiya, dabarar haka shine kokarin gajiyar da makaman kakkabo makamai masu linzami. Idan kasashen Amurka da Israila su ka yi ta amfani da wadannan makamai wajen kakkabo makaman Iran, cikin yan kwanaki zasu karar da irin wannan makamai nasu. Kuma har yanzu Iran bata fara aika muggan makamanta irinsu FATTAH-2 ba.
Iran ta kuma kai hare-hare a kasar Dubai a wurare masu mahimmanci, kamar kusa da Burja Khalifa, tashar jirgin ruwa da wasu wurare abinda ya kawo tsaiko ga hada-hadar kudade da kuma tsaida zirga-zirgar jirage a filin Jirgin sama mafi yawan fasinja a Duniya. Wadannan hare-hare sun tsayar da zirga-zirgar jirage ba kawai a gabas ta tsakiya ba, a duk fadin Duniya, kama daga Asia, Turai da Amurka sakamakon soke sauka da tashi a duk fadin yanki.
Sannan Iran ta rufe mashigin ruwa na Hormuz, abinda tabbas zai girgiza tattalin arzikin Duniya sakamakon kaso 25% na man da ake amfani da shi a Duniya daga nan yake wucewa. A kullum ana asarar litar Mai biliyan 3.1 (20 million barrels) wanda kasashen Gulf su ka dogara da shi. Nan da yan kwanaki gangar mai na iya haura Dala $150-200. Hakan kuma zai gurgunta tattalin arzikin Duniya gaba daya a shiga ‘recession’.
Idan yakin ya ci gaba, za a zo lokacin da Iran za ta fara amfani da manyan makamanta, bayan baturan kakkabo makamai sun karar da kayan aikinsu, sannan babu babbar tashar sansano makamai. Me ku ke tsammani idan aka kai ga haka?
Allah ya kawo karshen wannan yaki da gaggawa kuma ya baiwa Iran nasara domin su aka hara babu gaira babu dalili. Allah kuma ya umarci musulmi da cewa; ƙ22:3; “An yi izni ga waɗanda ake yãƙar su da cewa lalle an zãlunce su, kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa, Mai ĩkon yi ne a kan taimakonsu.”
Malam Ali Abubakar manazarci ne mazaunin Kano
