‘
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Mutane 14 ‘yan bindiga suka kashe a wani tagwayen hare hare da suka kai a ƙananan hukumomi biyu de ke jihar Katsina a yammacin Talata da ya wuce.
‘Yan bindigan sun kai mummunan harin ne a garin Ɗansoda da ke ƙaramar hukumar Ɗandume a lokacin da al’ummar garin suka kammala buɗe baki bayan gudanar da azumin watan Ramadan, inda rahotanni suka tabbatar da rasuwar mutane 14 tare da raunata wasu da dama.
A cewar mazauna yankin, maharan sun afka garin ne cikin dare, inda suka riƙa harbe-harbe ba ƙaƙƙautawa, lamarin da ya janyo firgici da tashin hankali a tsakanin al’ummar garin.
Harin ya zo ne a daidai lokacin da al’ummar garin suka kammala ibada da hutawa bayan wahalar yini ta azumi da suka sha.
Rahotanni sun ce baya ga waɗanda suka rasa rayukansu, mutane da dama sun samu mummunar raunuka, yayin da mutanen garin ke ci gaba da bincike domin gano ko maharan sun yi awon gaba da wasu daga cikin mazauna garin.
Wannan lamari ya jefa al’ummar yankin cikin alhini da takaici, inda mutane da dama ke bayyana harin a matsayin babban zalunci ga bayin Allah masu zaman lafiya,
duba da zaman sasanci da akayi dasu a baya.
Tuni aka gudanar da jana’izar waɗanda suka rasu waɗanda suka sami raunuka suna asibiti ana kulawa da su.
A garin Jiƙamshi da ke ƙaramar hukumar Musawa mutane uku ‘yan bindigan suka kashe sun raunata da dama.
‘Yan bindigan da sun kai hare haren da yammacin Talata lokacin da al’ummar yankin suna gama buɗe baki bayan suma sun gudanar da azumin watan Ramadan.
Rundunar ‘yan sanda a Katsina sun tabbatar da afkuwar hare haren a garin Jiƙamshi na ƙaramar hukumar Musawa.
Jami’in hu’ɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya tabbatar da mutuwar mutane 3 wasu 14 kuma suka sami raunuka a garin Jiƙamshi.
Ya bayyana cewa kwamishinan ‘yan sanda yayi Allah wadai da harin da yan bindiga suka kai a garin, ya kuma tabbatar da cewa yan sanda za su gudanar da bincike domin gano waɗanda suka aikata hare haren.
