Da Ɗumi-Ɗumi: Iran ta janye tawagar ‘yan ƙwallonta daga shiga Kofin Duniya na 2026

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kasar Iran ta sanar da cewa tawagar ‘yan ƙwallon ƙafarta ba za ta shiga sahun waɗanda su fafata ba a gasar Kofin Duniya na 2026, inda ta ce ta ɗauki matakin ne sakamakon yaƙinta da Amurka/Isra’ila da ake cigaba da gwabzawa.

Ministan Wasannin ƙasar, Ahmad Donyamali ya bayyana haka a wata hira da babban gidan talabijin na ƙasar a yau Laraba.

Ya ce, sun janye daga shiga gasar ne saboda faɗaɗar fargaba bayan kisan jagoran addinin ƙasar, Ali Khamenei a farkon yaƙin.

Za a gudanar da gasar, wadda aka faɗaɗa adadin ƙasashen da za su fafata zuwa 48, a tsakanin 11 ga watan Yuni da 19ga Yuli, a ƙasashen Amurka, Mexico da Kanada.

Iran ta haye zuwa zagaye na gaba ne bayan ta ƙara a mataki na ɗayan biyun sama a rukunin A na ‘yan Nahiyar Asiya.

A cewar ministan, halin da ake ciki a game da yaƙin ya sa suka ganin ba zai yiwu ‘ya’yan nasu su shiga gasar ba saboda rashin tabbas na tsaron rayukansu.

By Babaji