
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
‘Yan ta’adda da dama sun rasu yayin da dakarun tsaron Nijeriya suka sake karɓe iko da sansani atisayensu na garin Ngoshe da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza a Jihar Borno.
An gudanar da atisayen ne bisa haɗin-gwiwar jami’an haɗaka na CJTF da ‘yan sa kai da mafarauta.
A makon dau a gabata ne mayaƙan Boko Haram suka halaka sojoji 14 da fararen hula da dama a wani mummunan hari da suka kai wa yankin, inda kuam siak yi awon-gaba da sama da mata 100 da yara.
A cewar wata majiyar tsaro, da fari a ranar Juma’a ne Kwamanda Janar na rundunar (GOC) ya je Pulka, inda ya haɗa kan jami’ai guda 200 zuwa Ngoshe tare da duba halin da ake ciki a yankin.
Majiya ta ce sojojin sun yi nasarar ƙwato yankin daga hannun mayaƙan duk da cewa daga bisani sun (mayaƙan) kitsa mayar da martani a lokacin da suka yi cincirindo, saidai ƙarfin dakarun tsaron ya kere nasu, wanda ya sa suka jada baya.
Acikin mako guda an ruwaito cewa kwamandojin soji masu muƙamin laftanal kanal ne suka rasa rayukansu a hare-haren ‘yan ta’adda a Borno.
