
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rahotanni sun bayyana cewa wani ɗan Najeriya na cikin mutanen da suka samu rauni sakamakon harbo wasu makamai masu linzami da Iran ta yi zuwa Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE).
Hukumomin UAE sun ce rundunar tsaron sararin samaniyar ƙasar ta yi nasarar kakkaɓo wasu daga cikin makaman da Iran ɗin ta harba.
Wannan al’amari ya haddasa fargaba da jikkata mutane da dama, ciki har da ɗan Nijeriyar.
A cewar bayanin da gwamnatin UAE ta fitar a ranar Talata, tsarin tsaron sararin samaniyar ƙasar ya gano kimanin makamai masu linzami 262 da Iran ta harba tun bayan fara rikicin a ranar 28 ga Fabarairu, 2026.
Rahotanni sun ce Iran na kai hare-haren ramuwar gayya ne kan zargin cewa UAE ta bai wa Amurka damar amfani da wasu sansanonin sojinta da ke yankin Tekun Fasha domin kai mata (Iran) farmaki.
Haka kuma, hukumomi sun ce suna cigaba da sanya ido akan al’amuran tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, yayin da ake ƙoƙarin tantance adadin mutanen da harin ya shafa.
