Bauchi: ‘Yan bindiga sun sako amarya da mahalarta biki bayan karɓar fansar miliyan N25

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

‘Yan bindiga sun sako mutane 16 da suka yi garkuwa da su a lokacin hidimar bikin aure a Ƙaramar Hukumar Tafawa Ɓalewa ta Jihar Bauchi bayan an biya su fansar Naira miliyan 25.

Daga cikin waɗanda abin ya shafa akwai wata amarya da ‘yan tawagarta, waɗanda suka shafe kwanaki 57 a komar ‘yan bindigar kana aka sako su bayan biyan kuɗin fansar da ƙyar.

A ranar 10 ga watan Junairu aka yi awon-gaba da shi a bikin, wanda ya ƙunshi iyalan wani Malam Abubakar Santuraki Ubandoman Lim na garin Gwammadaji da ke Gundumar Dull a ƙaramar hukumar.

A cewar wata sanarwa da Bakiru Hassan Maga ya fitar a madadin Ƙungiyar Ci-gaban Gwammadaji, al’amarin ya faru ne a sa’ilin da tawagar ke yi wa amaryar rakiyar kai ta ɗakin mijinta da ke Dogo Yeli na Gundumar Bachama a Ƙaramar Hukumar Karim Lamiɗo ta Jihar Taraba.

An ruwaito cewa dukkanin waɗanda aka sace ‘yan ƙauyukan Gwammadaji, Wurno da Burga ne na Tafawa Ɓalewa a Bauchi.

Ƙungiyar ta bayyana cewa harin ya jefa ‘yan yankin cikin firgici da ƙuncin rashin sanin halin da suke ciki duba da cewa sun shafe kusa watanni biyu a hannun ‘yan bindigar.

By Babaji