Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Wata ‘yar kasuwa mai sayar da abinci a tashar motar Daɗin Kowa da ke garin Gombe, Hajiya Hauwa Inuwa, ta roƙi gwamnatin jihar da ta sake buɗe tashar, tana mai cewa rufe ta na tsawon lokaci ya jefa ‘yan kasuwa da direbobi cikin matsananciyar wahala.
Hajiya Hauwa, wacce ta shafe shekaru tana gudanar da sana’ar sayar da abinci a tashar, ta ce rufe tashar na kusan watanni goma ya kawo koma baya mai yawa ga rayuwar iyalai da dama da ke dogaro da harkokin da ake yi a wurin domin samun abin dogaro.
Ta bayyana cewa kafin a rufe tashar, wurin ya kasance cibiyar kasuwanci mai cike da harkoki, inda direbobi, fasinjoji da ‘yan kasuwa ke gudanar da mu’amaloli na yau da kullum da ke taimakawa wajen bunƙasa tattalin arzikin yankin.
“Tun bayan da aka rufe tashar motar, sana’ar mu ta samu koma baya sosai. Yawancin mu da muke sayar da abinci da sauran kayayyaki ga direbobi da fasinjoji yanzu muna fuskantar matsananciyar wahala wajen rayuwa,” in ji ta.
A cewarta, da dama daga cikin ‘yan kasuwa suna fuskantar matsaloli wajen biyan kuɗin haya, sayen kayan sana’a da kuma ciyar da iyalansu sakamakon raguwar kwastomomi.
Ta ƙara da cewa rufe tashar ba wai ‘yan kasuwa kaɗai ya shafa ba, har ma da direbobi, ma’aikatan sufuri da sauran ƙananan ‘yan kasuwa da harkokinsu ke da alaƙa da ayyukan tashar.
“Abincin da muke sayarwa a tashar shi ne babban abin dogaron mu. Ta wannan sana’a muke kula da iyalan mu da biyan buƙatun mu na yau da kullum. Amma yanzu mutane da dama sun rasa hanyar samun kuɗin shiga,” in ji ta.
Don haka ta yi kira ga gwamnatin jihar Gombe da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki da su duba wannan lamari tare da sake buɗe tashar domin rage wahalhalun da jama’a ke fuskanta.
Ta ce buɗe tashar motar Daɗin Kowa zai taimaka wajen farfaɗo da harkokin kasuwanci tare da bai wa ‘yan kasuwa da direbobi damar komawa sana’o’insu, lamarin da zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin al’umma a jihar.
