Hon. Datti Kura ya raba tallafin abinci a mazaɓarsa

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano 

Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Kura, Madobi da Garun Malam a Majalisar Wakilai, Hon. Yusuf Umar Datti Kura, ya raba kayan tallafin abinci na miliyoyin naira ga al’ummar mazaɓunsa domin rage musu radadin halin kunci, musamman a wannan lokaci na watan azumin Ramadan.

An gudanar da rabon tallafin ne a dakin taro na Hafizun Eɓent Center da ke Na’ibawa a Kano, inda dubban jama’a daga kananan hukumomin ukun suka halarta.

Da yake jawabi yayin kaddamar da rabon tallafin, Hon. Datti Kura ya bayyana cewa kimanin mutane 10,000 ne za su amfana da shirin tallafin daga ƙananan hukumomin da yake wakilta.

A cewarsa, duk wanda ya rabauta da tallafin zai samu buhun shinkafa, katon taliya da kuma kuɗin cefane, domin taimaka musu wajen gudanar da ibadar azumi cikin sauƙi.

Dan majalisar ya kuma yi kira ga al’ummar mazabarsa da su ci gaba da marawa tafiyar Kwankwasiyya baya, domin a cewarsa hakan ne zai taimaka wajen ci gaba da amfana da romon dimokuraɗiyya.

Ya ƙara da cewa duk da ƙalubalen siyasa da yake fuskanta, musamman kasancewar shi kadai ne ya rage daga cikin zaɓaɓɓun shugabannin yankin na jam’iyyar NNPP, hakan ba zai sa ya yi kasa a gwiwa wajen sauke nauyin da al’ummar mazabarsa suka dora masa ba.

Haka kuma ya gargaɗi waɗanda suka amfana da tallafin da su yi amfani da shi yadda ya dace, tare da kira gare su da su ci gaba da yi wa jam’iyyar NNPP addu’ar samun nasara a zaɓuka masu zuwa.

A nasu bangaren, wasu daga cikin jagororin al’umma daga ƙananan hukumomin Kura, Madobi da Garun Malam, sun nuna farin cikinsu da wannan tallafi.

Cikin waɗanda suka yi jawabi akwai Alhaji Saifullahi Mudansir Ibrahim daga Garun Malam, Alhaji Ado Hassan Ashafalala daga Kura, da Malam Muhammad Sabiu Kwankwaso daga Madobi, waɗanda suka yaba da ƙoƙarin ɗan majalisar.

Sun bayyana cewa tallafin ya zo a daidai lokacin da al’umma ke bukatar taimako, tare da jaddada cewa al’ummar yankin za su ci gaba da mara wa Hon. Datti Kura baya.

Haka kuma sun bayyana shi a matsayin jagoran da ke kokarin sauke nauyin da aka dora masa, tare da alƙawarin cewa al’ummar mazaɓar za su ci gaba da goyon bayansa a zaɓukan da ke tafe.

By ukarofi