Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
Kungiyar El-Rufa’i Support Group ta gudanar da wata zanga-zangar lumana a Kano domin nuna rashin jin dadinta kan tsare tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma jagoran jam’iyyar ADC na kasa, Malam Nasir El-Rufa’i.
Mambobin kungiyar sun bayyana cewa har yanzu hukumomin da ke tsare da El-Rufa’i ba su fito fili sun bayyana laifin da ake tuhumarsa da shi ba.
Da yake jawabi ga manema labarai a ofishin jam’iyyar ADC da ke Kano, daya daga cikin jagororin kungiyar kuma mai neman tsayawa takarar majalisar dokokin jihar Kano a karamar hukumar Tarauni, Hon. Aminu Nuraddeen Amin, ya ce makasudin zanga-zangar shi ne nuna rashin amincewarsu da yadda aka tsare jagoransu.
Ya ce abin da ke ba su mamaki shi ne yadda hukumar ICPC ta gayyaci El-Rufa’i, wanda ya amsa gayyatar domin girmama doka, amma daga bisani aka tsare shi ba tare da gurfanar da shi gaban kotu ko bayyana zargin da ake yi masa ba.
A cewarsa, kungiyar na duba yiwuwar garzayawa kotu idan har ba a gaggauta sakin jagoran nasu ko gurfanar da shi gaban kotu domin a fayyace tuhumar da ake yi masa ba.
Ya ƙara da cewa tsare shi na tsawon lokaci ba tare da bayani ba wani lamari ne da ke haifar da damuwa ga magoya bayansa.
A nasa ɓangaren, Shugaban jam’iyyar ADC na jihar Kano, Hon. Musa Shuaibu Ungogo, wanda ya karɓi baƙuncin masu zanga-zangar a ofishin jam’iyyar, ya bayyana El-Rufa’i a matsayin ɗan ƙasa nagari mai kishin al’umma.
Ya ce jam’iyyar ADC za ta ci gaba da gwagwarmayar siyasa domin tabbatar da adalci da inganta dimokuraɗiyya a Nijeriya.
Ungogo ya kuma yi kira ga al’ummar kasa da su fito su yi rijistar katin zaɓe domin su samu damar zaɓar shugabannin da suke so a zaɓukan da ke tafe.
Haka kuma ya jaddada cewa jam’iyyar ADC ba za ta lamunci siyan kuri’u ko amfani da kayan jawo hankalin masu kada kuri’a ba, yana mai gargaɗin duk wanda aka samu da aikata irin wannan laifi zai fuskanci hukunci.
A ƙarshe, shugaban jam’iyyar ya yaba wa mambobin ƙungiyar El-Rufa’i Support Group bisa shirya zanga-zangar lumana domin nuna damuwarsu kan abin da suka kira rashin adalci ga jagoransu.
