Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ƙi amincewa da bukatar Kwamishinan Kuɗi na Jihar Bauchi, Yakubu Adamu, na neman izinin tafiya zuwa Makka a ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji.
Mai shari’a Emeka Nwite ya yanke hukuncin ne a ranar Litinin, inda ya ce wanda ake tuhuma da laifin harkallar kuɗi har Naira biliyan 4.65 bai gabatar da isassun hujjoji a gaban kotu da za su tabbatar da bukatar tafiyar ba.
A hukuncin da Manhaja ta tabbatar a ranar Talata, alƙalin ya goyi bayan ƙorafin da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta gabatar, cewa takardar rantsuwar da aka haɗa da bukatar na da matsala saboda mai neman izinin bai sanya hannu a kanta ba.
Alƙalin ya ce takarda da ba sa hannu ba ta da wata ƙima a gaban doka, don haka ba ta cika mafi ƙarancin sharuddan da doka ta tanada ba.
Ya kuma ƙara da cewa duk da cewa kotu na girmama haƙƙin ɗan ƙasa da kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 ya tanada a sashe na 36, amma irin waɗannan haƙƙoƙi ba su da cikakken iko a kowane hali.
Mai shari’a Nwite ya kuma bayyana cewa shari’ar tsohon gwamnan Jihar Delta, James Ibori, wadda Mr Adamu ya ambata domin tallafa wa bukatarsa, ba ta dace da wannan shari’ar ba.
A cewar alkalin, Ibori ya nemi izinin tafiya ne bisa dalilan rashin lafiya, sabanin wannan bukata da ta shafi aikin ibada.
EFCC ta gurfanar da Mr Adamu a gaban kotu a ranar 30 ga Disamba na shekarar da ta gabata, bisa zargin wanke kuɗi har Naira biliyan 4.65.
An gurfanar da shi tare da kamfaninsa na haɗin gwiwa, Ayab Agro Products and Freight Company Ltd, kan tuhume-tuhume guda shida da suka haɗa da hade baki, wanke kuɗi, da kuma mallakar kuɗaɗen da ba bisa ƙa’ida ba.
Sai dai waɗanda ake tuhumar sun musanta dukkan zarge-zargen da ake musu.
A ranar 2 ga Fabrairu, Mai shari’a Nwite ya ba kwamishinan belin Naira miliyan 500, tare da sharaɗin samun masu tsaya masa guda biyu.
A cikin bukatar da ya gabatar, Adamu ya roƙi kotu ta ba da umarnin a sako masa fasfot ɗinsa domin ya samu damar tafiya zuwa Makka domin aikin Hajji, tare da dawowa Nijeriya kafin 21 ga Maris.
Takardar rantsuwar da Emmanuel Tsebo, sakataren shari’a a kamfanin lauyoyi na Chris Uche SAN & Co, ya gabatar a madadinsa ta tuna cewa kotu ta riga ta bayar da belin Adamu, tare da umartar a ajiye fasfot ɗinsa a hannun mataimakin babban magatakardar kotu domin tsaro.
Sai dai ya bayyana cewa kwamishinan na da buƙatar gaggawa ta zuwa Makka domin aikin ibada.
Adamu ya ce gudanar da aikin Hajji muhimmin ɓangare ne na addinin Musulunci, kuma ya yi alkawarin cewa zai dawo da takardun tafiyarsa zuwa kotu kafin 22 ga Maris tare da ci gaba da halartar shari’arsa.
Ya kuma roƙi kotu ta amince da bukatar, yana mai cewa hakan ba zai kawo cikas ga masu gabatar da ƙara ba, tare da cewa a yi hakan domin tabbatar da adalci.
Za a ci gaba da sauraron shari’ar a wani lokaci da kotu za ta bayyana.
