Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, a ranar Asabar ya yi wa ‘yan jam’iyyar adawa shaguɓe tare da bayyana su a matsayin waɗanda ba su shirya wa zaɓe ba. Ya kuma yaba wa shugaba Tinubu da jam’iyyar APC kam yadda ta mamaye ko’ina.
Akpabio ya yi wannan kalamai ne a yayin filin wasan Godswill Akpabio da ke Uyo a jihar Akwa Ibom a lokacin wani taro da uwargidan shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu, ta halarta albarkacin ranar mata ta duniya ta 2026.
A yayin da yake jawabi, shugaban majalisar ya ce ‘yan jam’iyyar adawa kansu na ci gaba da zama a rabe wanda ko kaɗan ba za su iya ƙalubalantar APC ba a zaɓen 2027.
“A wajena, ina nan. Idan muka yi doka, wasu sukan yi dariya wasu kuma su haɗe rai. Amma a duk san da na ga ɗan adawa ya haɗe rai, sai na ji daɗi, na san na yi dokar da ta dace kenan,” ya faɗa.
Akpabio ya ce, ‘yan jam’iyyar adawa suna fama da rashin tsari a jam’iyyunsu a yayin da APC ke ci gaba ƙarfi a faɗin ƙasar nan.
“Saboda a yayin da muke zaga Nijeriya muna tuntuɓa da yaƙin neman zaɓe, wasu kuma a lokacin suke kafa jam’iyyar.”
“Ba su ma gama rajista ba, kuma haka za su cigaba da tafiya cikin ruɗu har zuwa a gama zaɓen 2027. A maimakon haɗa kansu, kan nasu sai rarrabuwa yake.”
Ya kuma buga misali da rikicin da jam’iyyun LP da PDP ke fama da shi.
Sannan Akpabio ya yi watsi da barazanar wasu ‘yan siyasa na ƙaurace wa zaɓe saboda gyaran dokar zaɓe da aka yi.
“A jiya, Na ga wani mutum yana ihu a talabijin saboda an yi gyaran dokar zaɓe, yana cewa za su iya ƙauracewa zaɓe. Sai na ce masa ya dai faɗi gaskiya, zai ƙaurace wa zaɓe ne saboda ba su shirya ba,” ya faɗa ba tare da kama sunan kowa ba.
Shugaban majalisar dattawa ya yaba wa shugaba Tinubu kan gina jam’iyya mai ƙarfin gaske.
“Ina son na taya shugaba Tinubu murna Bola Tinubu kan yadda ya kafa jam’iyya mai ƙarfi. APC, da yadda ya iya riƙe cikin tsari har ya zama tana da gwamnoni 31 kuma ana ta samun ci gaba.”
“Idan dai siyasa abu ne na al’umma, shin za ka iya doke wannan mutumin kuwa?” Akpabio ya tambaya.
Kalaman Akpabio na zuwa ne a yayin da ake tsaka da dambarwar gyaran dokar zaɓe a Nijeriya, musamman tanadin dokar tura sakamakon zaɓe kai tsaye ta intanet.
Wanann jarida ta rawaito muku yadda ‘yan majalisar wakili suka yi wasu da tura sakamakon kai tsaye ta intanet daga rumfunan zaɓe duk da irin kiraye-kiraye da ƙungiyoyin al’umma suka yi.
Masu suka dai na ganin ƙin yin hakan zai tauye sahihancin zaɓe da ƙarya ƙarfin guiwar da al’umma ke da shi a zaɓe musamman kan irin dambarwar da ta biyo bayan zaɓen 2023.
Masu goyon bayan gyaran na ganin cewa ya kamata hukumar zaɓen ta ci gaba da amfani da tsowon tsarin amfani da takarda wajen rubuta sakamakon zaɓe baya ga tura sakamakon kai tsaye ta intanet musamman idan aka samu gazawar netwok.
