Don al’umma zan tsaya takara, ba don ƙalubalantar Fintiri ba – Buba Kwacham

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Alhaji Abdulrahaman Buba Kwacham ba baƙon suna ne a kafafen yaɗa labarai ba, kasancewarsa gogaggen ɗan siyasa kuma jigo a Jam’iyyar APC, musamman a Jihar Adamawa da Arewa bakiɗaya. Shine Sarkin Fulanin Mubi kuma Shugaban ƙungiyar ‘Movement for North East’. A ’yan kwanakin nan ne aka samu cece-kucen siyasa tsakaninsa da Gwaman Jihar Adamawa, Alhaji Ahmadu Fintiri, wanda kwanan nan ya canza sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC, inda ya yi wasu maganganu da ake hasashen ya yi su ne akan Hon. Buba Kwacham. Da wannan ne Hon. Kwacham ya tattauna da Blueprint Manhaja, don fahimtar da al’umma gaskiyar zance da kuma niyyar da ke cikin maganganun da ya yi, wanda shi gwamna ya ga kamar don shi ya yi su.

MANHAJA: A baya-bayan nan Gwanman Jihar Adamawa ya yi wasu batutuwa da ake hasashen ma da kai yake, inda ya bayyana ka a matsayin wanda ke barin jam’iyya daga nan zuwa can, don ba ka samun nasara, kai kuma ka ƙalubalance shi kan cewa, zai canza sheƙa zuwa APC ne don ya ƙwace ta a matsayin jagoranta bayan ku Nuhu Ribadu ku ka sani. Shin me za ka ce?

KWACHAM: To, alhandulillahi, ka san an ce, magana zarar bunu ce, koda yake ya ce don mutum ya iya Hausa ba shine wani abu ba. Abu na farko na yi imani da Allah kuma muna cikin wata na Ramadana, ban taɓa a duniya na ce na saukar wa wani ko na bar wa wani tun da na fara siyasa ba. Kuma canza jam’iyya kamar yadda na sha faɗa ita jam’iyya riga ce, za ka iya sauya ta a duk lokacin da ka ga dama. Amma wallahi! wallahi! ni Musulmi ne, ban taɓa bar wa wani muƙamin da aka ce na bar masa ba na shiga wata jam’iyya. Idan kuwa har akwai ya fito ya musanta zancena, ya tabbatar tsakaninsa da Allah zai bayyana cewa na taɓa bar wa wani takara ko sau ɗaya ne. Kuma abu na biyu duk wani ɗan siyasa indai a Nijeriya ne kuma ya taka wani matsayi kawo wa yanzu ba wanda zai taɓa buga ƙirji kan cewa bai taɓa canza jam’iyya ba, ko shi karan kansa gwamnan, domin jam’iyyar da ya fara tsaya wa takara ba PDP ba ce, a ACN ya fara tsayawa. Yanzu kuma yana son ya shiga APC. Magana ta biyu, ni ban yi magana da shi ba, ban kuma zage shi ba, jam’iyyata nake gargaɗi kan irin waɗannan abubuwa da take yi, sai shi ya tsargu. Wasu suna ganin cewa, Gwanma Fintiri ya fito daga yanki nawa ne shi ya sa nake ta faɗa, to fa ga masu faɗan haka, tabbas za mu yi shari’a da su a gaban Allah. A je a tambaye shi Gwaman Fintiri, a ranar 1 ga watan Oktoba (2025) ya muka yi da shi ga gidan gwamnati? Wasu mutane na cewa wai don shi gwamna na neman sanata ni ma Ina nema, kuma mun fito daga yanki ɗaya ne ya sa nake waɗannan maganganu, ku tambaye shi muna tare a ranar ta 1 ga watan Oktoba, ni ne na fara ce masa ya nemi kujerar sanata, don ba ni da ra’ayin. Banda shi ma mutane da yawa na ba su wannan shawarar, kuma wasu daga cikinsu Allah ya taimake su ya ba su wasu matsayi. Na san da yawan mutane na ganin ana laƙa hotuna na kan zan tsaya takara, magana ta haƙiƙa mutane ne ke sakawa suna kira gare ni don na tsaya takara, amma ban yi niyya ba. Sai dai a yau 9 ga watan Ramadana Ina mai shaida muku cewa zan tsaya takarar sanata. Duk da haka Ina ƙalubalantar gwamna ya fito ya sanar da jama’a ni ban ce masa ya tsaya takarar sanata ba.

Amma ya yi zargin ka da cewa kai mutum ne da ya fi ƙarfi a hargowar siyasa, ba ka cin zaɓe ko ka tsaya. Shin me za ka ce kan hakan?

Siyasar da na tsaya a SDP, na samu ƙuri’u 19,700, wanda wani gwamna a jiharsa da su yake cin zaɓe. Kuma ruwa wannan na leda ban san na ba wa talaka don ya zaɓe ni ba. Shi da yake wannan maganar, ya fito ya sanar da ni duk Nijeriya waye ubangidana da ya ke taimako na don na ci siyasa. Abu na farko a Jam’iyyar ACN idan bai manta ba Halid Mahmood shi ya kawo shi ya goya masa baya aka tsayar da shi. Magana ta biyu, ya zo ya tsaya mamba a PDP, ni Kwacam na taimake shi. Duk wanda ke musun haka ya je ta tambaye Inyaku yana nan da rai, wacce gudunmuwa na bayar a lokacin. Harwayau da ya zo takarar gwamna, na taimake shi. Boni Haruna yana nan, Musa Garba yana nan, Umar Liman yana nan, duk shaida ne kan irin gudunmawar da na bayar. ɓangaren gudunmawa ta kuɗaɗe, na taimake shi matuƙa, ina so mutane su san da wannan. Kai har wannan zaɓe na ƙarshe shi ma na ba shi taimako fiye da tunani. Bayana ya ci zaɓe shi da kansa ne ya mani ƙorafin bana zuwa Gidan Gwamnati. Da na je na gaya ma shi bana buƙatar ko Naira daga wurinsa. Idan ya taɓa ba ni kuwa ya faɗa duniya ta ji. Na sanar da shi ina so dai ya ba ni kason al’ummata na ba su, kuma ya ce zai yi hakan, kuma na san zai yi ɗin tunda ya ce, muna kan haka ne wannan abun ya samu. To saboda kar na rasa abin da na nema sai na ƙi faɗar gaskiya.

To, ko akwai wani tsoro da kuke ji a matsayinku na jam’iyyar APC a Adamawa na shigar Gwamna Fintiri jam’iyyar?

Wane irin tsoro mu ke ji? Na ce fa ni da kaina na ce masa ya kamata ya nemi kujerar sanata. Wane irin tsoro za mu ji nasa? Ya fa yi gwamna na shekaru takwas yana shirin ƙarewa a ‘yan watanni masu zuwa.

Shin za ka tsaya takara ne don ka ƙalubalanci gwamna mai ci ko kuwa?

Abu na farko da zan sake nanatawa shine ni ba ni da sha’awar yin takara a karan kaina, idan aka duba duk tallace-tallacen da ake saka wa na takarar tawa wasu ne ke yi ba ni ba. Kuma ƙungiyoyi da dama sun zo har wurina suna neman in tsaya takara. Kuma abinda na ke gaya masu shi ne mu nemi zaɓin Allah. Don haka adawa da shi na me zan yi. Yau idan ya fito takara, na fito takara, idan shi Allah ya ba tsakani da Allah zan tsaya in ba shi taimako daidai ƙarfina. Don haka domin al’umma zan yi takara, ba ƙalubalantar gwamna ba.

Shin ba kundin tsarin jam’iyya ne ya bada dama ga gwamna ya zama jagoran jam’iyya a jiha ba?

Abinda nake magana ba, shin tsarin jam’iyya ba hannu ne ya rubuta shi ba? Ko daga sama ya sauko? Ni kuma Ina kira ne ga shuwagabannin jam’iyyata ne fa, ban kira Gwamna Fintiri ba kan maganar ba. Kirana a jam’iyyar yake.

A ƙarshe me kake son a yi a samar da masalaha?

Ni ba na son komai. Idan ma za a ɗauki jam’iyyar a miƙa ta ga hannun Gwamna Fintiri, ba zai dame ni ba. Damuwata kawai waɗanda suka yi wahala a jam’iyyar a tsayin waɗannan shekaru takwas, ni shine damuwata. Mutane su fahimta, ni ba ni da damuwa, damuwata mutanen da suka kwashe shekaru takwas suna bauta wa jam’iyyar da dukiyarsu da ƙarfinsu, wai a ce an waye gari sun zama ’yan kallo.

By ukarofi