Aƙalla mutane shida sun rasa rayukansu yayin da wasu uku suka jikkata sakamakon wata gobara mai muni da ta tashi a cikin wata bas a garin Kerzers da ke yammacin ƙasar Switzerland.
Hukumomin ‘yan sanda sun bayyana cewa gobarar ta faru ne a daren Talata, kuma akwai alamun cewa wani mutum a cikin bas ɗin ne ya janyo gobarar da gangan.
Kakakin ‘yan sandan yankin Fribourg, Frederic Papaux, ya ce binciken farko ya nuna cewa wani mutum da ke cikin bas ɗin na iya aikata wannan aiki da gangan.
Rahotanni daga wasu kafafen watsa labarai sun nuna cewa mutumin ya zuba fetur a jikinsa sannan ya kunna wuta, lamarin da ya haddasa gobarar da ta bazu cikin sauri.
Wani kakakin ‘yan sanda, Christa Bielmann, ta ce har yanzu bincike na gudana domin gano cikakken dalilin faruwar lamarin.
Sai dai ta jaddada cewa a halin yanzu babu wata shaida da ke nuna cewa lamarin na da alaƙa da ta’addanci.
Garin Kerzers na da yawan jama’a kusan 5,000 kacal, kuma yana kusa da babban birnin Switzerland wato Bern. Shaidu sun ce gobarar ta fara ne da ƙaramin wuta a cikin bas ɗin kafin ta rikiɗe zuwa babbar gobara cikin ƙanƙanin lokaci.
Wata ma’aikaciyar shago mai suna Mina Gendre ta ce ta ga yadda bas ɗin ta tsaya a hanya kafin gobarar ta tashi.
Ta ce, “Na ga wata ƙaramar wuta a cikin bas ɗin, amma cikin kusan rabin minti kawai sai ta zama babbar gobara.”
Ta kuma ƙara da cewa, ta ga wani mutum yana fitowa daga cikin bas ɗin jikinsa na ƙonewa.
Rahotanni sun ce wasu daga cikin fasinjojin bas ɗin sun yi ƙoƙarin tserewa daga gobarar yayin da wasu mutane a wajen suka yi ƙoƙarin taimakawa wajen kashe wutar da jaket ko wasu kaya.
Mutane uku da suka jikkata an kai su asibiti domin samun kulawa. Saidai wasu biyu daga cikin waɗanda suka samu rauni ba sai an kwantar da su a asibiti ba.
Hukumomi sun ce mutane shida sun mutu a gobarar, amma ana iya ɗaukar kwanaki kafin a gano ko su wane ne.
Har yanzu ba a tabbatar ko mutumin da ake zargin ya kunna wutar yana cikin waɗanda suka mutu ba.
Shugaban ƙasar Switzerland, Guy Parmelin, ya bayyana alhini matuƙa game da lamarin.
Imda yake cewa, “Wannan lamari ya girgiza zuciya, kuma yana da matuƙar ban tausayi ganin yadda aka sake rasa rayuka a wata gobara mai muni a Switzerland.”
Shugaban kamfanin bas ɗin Postauto, Stefan Regli, shi ma ya mika ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka mutu.
Wannan lamari ya sake tada hankalin jama’a a Switzerland saboda har yanzu ba a manta da wata gobara da ta faru a watan Janairu ba a wani mashaya a wurin yawon shakatawa na Crans-Montana, inda mutane 41 suka mutu yayin da fiye da 115 suka jikkata.
Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa irin waɗannan abubuwa ba su saba faruwa a ƙasar ba, amma sun fara zama ruwan dare a sassa daban-daban na duniya.
