Sallah: NRC ta ƙaddamar da aikin zirga-zirgar sufurin jiragen ƙasa domin sauƙaƙa wa matafiya

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Jiragen ƙasa ta Nijeriya (NRC) ta sanar da ƙaddamar da karin zirga-zirgar jiragen ƙasa a manyan hanyoyin sufuri a faɗin ƙasar nan domin sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a yayin bikin Eid-el-Fitr.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Callistus Unyimadu ya fitar, ya ce an ɗauki matakin ne domin samar da sufuri mai sauƙi, tsaro da inganci sakamakon karuwar matafiya da ake sa ran samu a lokacin bukukuwan Sallah.

Hukumar ta bayyana cewa za a ƙara yawan tafiye-tafiye a muhimman hanyoyi kamar Legas–Ibadan da Abuja–Kaduna domin biyan buƙatar jama’a.

A kan hanyar Legas–Ibadan, NRC ta ce za a gudanar da tafiye-tafiye na musamman guda uku a ranar 19 ga Maris, 2026, daga kowanne ɓangare na hanya. Jirage za su tashi daga tashar Mobolaji Johnson da ke Ebute Metta, Legas da ƙarfe 7:40 na safe, 1:40 na rana da 4:00 na yamma, yayin da daga tashar Obafemi Awolowo da ke Moniya, Ibadan za su tashi da ƙarfe 8:00 na safe, 10:50 na safe da 4:30 na yamma.

A kan hanyar Abuja–Kaduna kuwa, hukumar ta ce za ta gudanar da tafiya sau biyu a ranar 19 ga Maris, sannan daga ranar 20 zuwa 23 ga Maris za a rika gudanar da tafiye-tafiye sau uku a kowace rana domin bai wa matafiya damar zabi lokaci.

Haka kuma NRC ta bayyana haɗin gwiwa da gwamnatin jihar Osun wajen gudanar da jirgin ƙasa na musamman mai suna “Imole Special Train,” wanda zai ɗauki ’yan asalin jihar daga tashar Iddo da ke Legas zuwa Osogbo kyauta. Ta ce gwamnatin jihar Osun ce ke ɗaukar nauyin shirin, yayin da NRC ke bayar da kayan aiki da kuma kula da gudanar da aikin.

Bugu da ƙari, hukumar ta ce zirga-zirgar jiragen ƙasa a hanyar Warri–Itakpe za ta ci gaba da gudana sau uku a mako kamar yadda aka saba, yayin da sabis ɗin Port Harcourt–Aba zai ci gaba da aiki yadda aka saba a lokacin Sallah.

A ƙarshe, NRC ta tabbatar wa jama’a da kudirinta na samar da sufuri mai aminci da inganci, tare da shawartar matafiya da su shirya tafiyarsu tun da wuri, su isa tashoshin jirgin da wuri, kuma su bi duk ƙa’idojin tikiti da tsaro domin guje wa cunkoso da tangarda.

By ukarofi