Gwamna Soludo ya sauke dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa a Jihar Anambra

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya sauke dukkan muƙarraban siyasa da ke aiki a gwamnatinsa, inda ya umarce su da su miƙa ragamar aiki ga sakatarorin dindindin ko kuma manyan ma’aikatan gwamnati mafi girma a ma’aikatunsu da hukumominsu.

Wannan mataki na zuwa ne kwana guda bayan rantsar da shi karo na biyu a matsayin gwamnan jihar.

A cikin wata sanarwa da Sakatare Dindindin na Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar, Nwabufo Nwankwo ya fitar, an umarci dukkan wadanda abin ya shafa da su kammala mika ragamar aiki kafin ƙarshen ranar Laraba, 18 ga watan Maris, 2026, ga jami’an da za su rike harkokin ofisoshin har zuwa lokacin da za a kafa sabuwar majalisar ministoci.

Sanarwar ta kuma buƙaci dukkan mambobin majalisar ministocin zangon farko da su halarci wani taro da gwamnan zai jagoranta a ranar Litinin, 23 ga watan Maris, 2026, da ƙarfe 10 na safe a dakin taro na ANSEC da ke Awka.

An rantsar da Soludo a karo na biyu a ranar Talata a wani biki da aka gudanar a sabon filin Aleɗ Ekwueme da aka gyara a babban birnin jihar, Awka, tare da mataimakinsa Onyeka Ibezim.

A jawabin da ya gabatar yayin bikin rantsuwar, gwamnan ya yi alkawarin kara kokari wajen yi wa al’ummar jihar hidima, yana mai bayyana cewa gwamnatinsa ta samu gagarumin ci gaba musamman a bangaren tsaro a cikin shekaru hudu da suka gabata.

Ya ce matsalar zaman gida (sit-at-home) ta ragu sosai, inda makarantu, kasuwanni da sauran harkokin yau da kullum suka koma yadda suke, yana mai cewa Anambra na daga cikin jihohin da suka fi samun tsaro a Nijeriya a halin yanzu.

By ukarofi