Gidauniyar Al-Ihsan ta raba tallafin abinci da kayan Sallah ga marayu da marasa ƙarfi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Gidauniyar Al-Ihsan ƙarƙashin jagorancin Dr. Hauwa’u Yakubu Bako ta gudanar da rabon tallafin kayan abinci da kayan Sallah ga marayu da marasa ƙarfi a wani ɓangare na ayyukan jinƙai da take yi lokaci-lokaci domin rage raɗaɗin rayuwa ga al’umma.

An gudanar da rabon tallafin ne a wani taro da ya gudanar a makarantar Yombe da ke Kurmin Mashi Kaduna, inda ya samu halartar masu ruwa da tsaki da kuma waɗanda suka amfana, inda aka raba kayayyaki da suka haɗa da shinkafa, wake, gero da kuma kayan sawa na Sallah domin bai wa waɗanda suka ci gajiyar damar gudanar da bukukuwan Sallah cikin walwala.

Da take jawabi yayin rabon tallafin, shugabar gidauniyar, Dr. Hauwa’u Yakubu Bako, ta bayyana cewa manufar wannan shiri ita ce tallafa wa marayu da marasa galihu musamman a irin wannan lokaci na Sallah, domin su ma su samu damar yin farin ciki kamar sauran al’umma.

Ta ƙara da cewa gidauniyar za ta ci gaba da ƙoƙarin faɗaɗa ayyukanta na jinƙai, tare da jaddada cewa kula da marasa ƙarfi na daga cikin muhimman ayyukan da ke kawo cigaba da daidaito a cikin al’umma.

Wasu daga cikin iyayen marayun da suka amfana da tallafin sun bayyana jin daɗinsu tare da miƙa godiyarsu ga gidauniyar bisa wannan taimako da suka ce ya zo a daidai lokacin da suke cikin buƙata.

A ƙarshe, Dr. Hauwa’u Yakubu Bako ta yi kira ga masu hannu da shuni da sauran ƙungiyoyi da su ƙara himma wajen tallafa wa marasa galihu, tana mai cewa haɗin kai ne kawai zai taimaka wajen rage talauci da inganta rayuwar al’umma baki ɗaya.

By ukarofi