Muhimmancin kare sirrin asusun banki a zamani mai cike da ’yan damfara

Spread the love

Gargaɗin da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi wa ’yan Nijeriya kan kare lambobin sirri, kalmomin shiga da sauran bayanan banki ba kawai saƙon faɗakarwa ba ne na yau da kullum, illa wata muhimmiyar kira ce ga jama’a su ɗauki mataki cikin gaggawa domin kare dukiyoyinsu. A wani lokaci da damfarar kuɗi ke ƙara yawaita tare da ɗaukar sabbin salo na zamani, sakaci da bayanan banki na iya jefa mutum cikin babbar asara cikin ƙanƙanin lokaci.

A yau, kusan duk mu’amaloli — daga biyan kuɗin abinci zuwa sayayya da kasuwanci — ana yin su ta hanyar fasahar zamani, wanda hakan ya sa tsaron bayanan sirri ya zama ginshiƙin tsaron kuɗi.

CBN ya sake jaddada wannan gargaɗi ne a lokacin bikin Makon Wayar da Kan Jama’a kan Mu’amalolin Kuɗi, wato Global Money Week 2026, inda ya tunatar da jama’a cewa babu wani banki ko jami’in banki na gaskiya da zai taɓa buƙatar kwastoma ya bayyana PIN ɗinsa, kalmar sirrinsa ko lambobin tantancewa ta waya, saƙon rubutu ko kafafen sada zumunta. Duk da haka, har yanzu ana samun mutane da dama da ke faɗawa tarkon masu damfara saboda rashin sani, sakaci ko kuma amincewa da saƙonnin ƙarya da ake turo musu cikin salo mai kama da na hukuma.

Abin damuwa shi ne yadda damfara ta kuɗi ta sauya daga tsohuwar zamba zuwa dabaru na zamani masu amfani da fasahar sadarwa. Wasu na kiran mutane suna gabatar da kansu a matsayin ma’aikatan banki, suna tsoratar da su da cewa asusunsu na cikin haɗari. Wasu kuma na aika saƙonnin imel, saƙonnin waya ko hanyoyin intanet da ke kama da shafukan banki na gaskiya. Da zarar mutum ya saka bayanansa a irin waɗannan hanyoyi, cikin ’yan mintuna kaɗan ana iya kwashe duk abin da ke asusunsa ba tare da barin wata alama ba. Wannan ya sa ilimi da wayar da kai suka zama kariya mafi ƙarfi fiye da kowace na’ura ko fasaha.

Dole ne jama’a su fahimci cewa tsaron kuɗi ba nauyin bankuna kaɗai ba ne. Haƙƙi ne na bai ɗaya tsakanin banki da kwastoma. Ko da bankuna sun samar da manyan tsare-tsare na tsaro, babu wata kariya da za ta yi tasiri idan mai asusun da kansa ya miƙa bayanansa ga wanda bai dace ba. A taƙaice, bayyana PIN ko kalmar sirri ga wani kamar buɗe ƙofa ne ga ɓarawo da gangan.

Har ila yau, wannan gargaɗi na CBN ya zo ne a lokacin da ake matuƙar buƙatar ƙarfafa ilimin kuɗi a tsakanin jama’a, musamman matasa da sabbin masu amfani da banki ta yanar gizo. Fahimtar yadda ake sarrafa kuɗi, gane dabarun damfara, da kuma sanin matakan kariya na iya ceton miliyoyin naira daga asara a duk shekara. Iyaye, makarantu, ƙungiyoyi da kafafen yaɗa labarai na da rawar takawa wajen yaɗa wannan ilimi domin gina al’umma mai wayewa a harkokin kuɗi.

A ƙarshe, gina tattalin arziki mai ƙarfi a wannan zamani na dijital ba zai yiwu ba tare da amincewa da tsarin banki ba, kuma wannan amincewa tana dogara ne da tsaro. Jama’a su kiyaye sirrinsu, bankuna su ƙara inganta tsare-tsare da faɗakarwa, hukumomi kuma su hukunta masu aikata damfara ba tare da sassauci ba. Waɗannan su ne ginshiƙan kare dukiyar ’yan ƙasa. A haƙiƙanin gaskiya, a yau sirrin bayanan banki ya zama sabuwar garkuwar kuɗi; duk wanda ya yi watsi da shi, ya bar ƙofar asara a buɗe.

By ukarofi