
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ministan Lantarki a Nijeriya, Adebayo Adelabu na shirin yin murabus daga muƙaminsa domin neman takarar gwamna a Jihar Oyo.
Hakan na zuwa ne bayan umarnin Shugaba Bola Tinubu na cewa wajibi ne dukkan waɗanda aka ba muƙamai a gwamnatinsa da ke son tsayawa takarar siyasa su ajiye aikinsu.
Matakin Adelabu na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da sukar matakin ƙoƙarinsa a kujerar ministan musamman bisa la’akari da gazawarsa ta rashin samar da megawat 6,000 na wutar lantarki a Nijeriya.
Hakan ya jefa fannin lantarki cikin ƙalubale da dama ciki har sa rashin samar da wadataccen wuta, matsalolin lalacewar rumbun ƙasa da rashin wadataccen rabawa.
A yanzu adadin ƙarfin samar da lantarki a Nijeriya na matakin megawat 3,331, wanda ya kasa da kaso mai girma daga cikin tsarin aikin Adelabu da dai sauran matsalolin da fannin ke fuskanta
Masu sharhi na ganin wanda zai gaje shi a muƙamin ka iya gadar manyan matsaloli da ke buƙatar agajin gaggawa, ƙarin kuɗaɗe, da kuma ƙarfin harkokin gudanarwa.
