‘Yan bindiga sun harbe ‘yan sanda uku da ɗan bijilante a Taraba

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kashe jami’an ‘yan sanda uku da wani jagoran ‘yan bijilante a yankin Tordamisa da ke Ƙaramar Hukumar Donga a Jihar Taraba.

Haka kuma, sun harbe wani ɗan shekara 60, wanda shi ne shugaban ‘yan bijilante a ƙauyen Tordamisa.

Rahotanni sun bayyana cewa al’amarin ya faru ne a wani hari da aka kai cikin dare, inda maharan suka afka wa al’ummar yankin ba tare da gargaɗi ba.

A yayin haka ne, ‘yan sanda uku da ke bakin aiki suka rasu yayin da suke ƙoƙarin kare al’umma da dukiyoyinsu.

Sannan, an halaka fararen hula guda biyar a harin, lamarin da ya jefa yankin cikin firgici da jimami.

Wasu majiyoyi sun ce, maharan sun kai farmakin ne ɗauke da muggan makamai, inda suka riƙa harbe-harbe ba ƙauƙautawa, lamarin da ya sa mazauna yankin suka tsere domin neman tsira.

Tuni dai jami’an tsaro suka isa wajen domin kwantar da hankula da kuma fara bincike akan yadda lamarin ya far da matakin damejin da ya yi.

Al’umma na kira ga hukumomi da su kara ɗaukar matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi, tare da tabbatar da cewa an kamo waɗanda suka aikata wannan aika-aika domin su fuskanci hukuncin da doka ta tanada.

By Babaji