
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta rattaɓa hannu akan wata yarjejeniya da Birtaniya wadda za ta bai wa Birtaniya damar mayar da dubban ‘yan gudun hijira da aka ƙi amincewa da su da kuma masu laifi zuwa Nijeriya.
An ƙulla yarjejeniyar ne a tsakanin Ministan Harkokin Cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, da Sakatariyar harkokin cikin gida ta Birtaniya, Shabana Mahmood a yayin ziyarar aiki da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kai wa ƙasar.
Hukumar kula da harkokin cikin gida ta Birtaniya ta bayyana cewa, yarjejeniyar za ta bada damar mayar da waɗanda aka ƙi ba su mafaka da kuma masu aikata laifuka zuwa ƙasarsu ta asali.
Wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Nijeriya da Birtaniya akan harkokin tsaro, hijira da kuma shari’a domin amfanin ƙasashen biyu.
Ana sa ran wannan yarjejeniyar za ta haifar da cece-kuce, musamman akan yadda za a kula da waɗanda za a dawo da su da kuma tasirin hakan ga tsarin tsaro da zamantakewar Nijeriya da al’ummarta.
