
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya buƙaci jagororin addinin Musulunci da su yi amfani da lokacin Ƙaramar Sallah waken yi wa Nijeriya addu’a na samun zaman lafiya da ci-gaba mai ɗorewa.
Tinubu ya bayyana haka ne a saƙonsa na barka da sallah, wanda Kakakinsa Bayo Onanuga ya fitar, inda a ciki ya yi kira da a ƙara ƙaimi wajen ƙaunar ƙasar da son juna.
Ya kuma buƙaci Musulman ƙasar da su cigaba da koyi da abubuwan da suka koya a watan Ramadana, wanda ya ƙarfafa “imani da tausayi da haɗin kai a tsakanin al’umma.”
“Akwai darussa da yawa da za mu koya daga watan Ramadan, musamman a wannan lokacin da muke ciki. Ya kamata mu ci gaba da amfani da darussan da muka ɗauko na taimakon juna da juriya da tausayi har bayan azumin na watan Ramadan,” in ji shi.
Kazalika, shugaban ya buƙaci Musulman ƙasar da su nuna ƙauna da son juna ta hanyar taimakon marasa galihu ba tare da la’akari da bambancin addini ba, domin a cewarsa, hakan ne zai ƙara haɗa kan ƴan ƙasa da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a tsakaninsu.
