Juyin mulki: Yadda aka zargi wasu da kitsa karɓe iko da Aso Rock da halaka Tinubu da wasu – Rahoto

Spread the love

An ƙara samun sababbin bayanai akan zargin yunƙurin da aka yi na kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu yayin da ake tsaka da bukukuwan Ƙaramar Sallah.

A ‘yan watannin baya ne dai aka fara jin ƙshin-ƙishin ɗin cewa wasu dakarun sojoji da hadin bakin wasu manyan mutane a Nijriya sun kitsa yi wa shugaban ƙasar juyin mulki, saidai asirinsu ya tonu gabanin aiwatarwa.

Jaridar Premium Times ta bankaɗo wasu sababbin bayanai da ke nuna cewa wasu da ake zargi da shirin juyin mulki sun tsara kai wani gagarumin hari domin ƙwace iko a Nijeriya.

“Binciken ya nuna cewa bayan shirin kashe su da aka ruwaito a baya, akwai wani tsari mai zurfi da waɗanda ake zargi suka tsara domin ƙwace Fadar Shugaban Ƙasa tare da rusa tsarin jagoranci na kasar”, kamar yadda jaridar Alƙibla ta ruwaito.

Rahotanni sun nuna cewa babban abin da suka sa gaba shi ne mamaye Fadar Shugaban Ƙasa, wato Aso Rock a Abuja, wadda ita ce cibiyar mulkin Nijeriya mafi tsaro, domin samun damar kama Tinubu da mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima.

Sannan, “an ce shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas suna cikin waɗanda ake shirin kamawa ko ma a kashe su”, inji rahoton jaridar.

Masu bincike sun ce shirin ya hada da kai hari kan manyan jami’an tsaro kamar mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribaɗu, tsohon sufeto janar na ‘yan sanda Kayode Egbetokun, da daraktan DSS, Adeola Ajayi.

An ce an ware wasu jami’ai na musamman da za su jagoranci kai hare-haren, ciki har da wata tawaga da aka kira “decapitation unit”, wacce za ta jagoranci rusa manyan shugabanni.

Rahotanni sun nuna cewa an tsara shirin ne kamar cikakken juyin mulkin soja, inda aka raba ayyuka ga tawagogi daban-daban domin ƙwace muhimman wurare a lokaci guda.

Yayin da wata tawaga za ta kai hari kan Aso Rock, wata kuma za ta ƙwace barikin Neja, wadda ke kusa da Fadar shugaban kasa kuma ke ɗauke da manyan hafsoshin soja.

A nan ne aka tsara kashe manyan hafsoshin soja ciki har da babban hafsan tsaro da shugabannin rundunonin soja.

Sauran tawagogin kuma an ba su umarnin kwace cibiyar rundunar sojojin Nijeriya da ke Garki a Abuja, da kuma filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, domin katse hanyoyin shiga da fita daga babban birnin.

Masu bincike sun ce, idan da wannan shiri ya yi nasara, da cikin ‘yan sa’o’i kaɗan masu shirin juyin mulkin za su mallaki ikon tafiyar da Abuja gaba daya, cewar rahoton Premium Times, kamar yadda Alƙibla ta wallafa.

By Babaji