‘Yan sanda sun kama mai gari da wasu kan shirya bikin bajekolin fyaɗe

Spread the love

Rundunar ‘yan sanda a Jihar Delta, ta kama wani jagoran al’umma kuma mai shirya wani taron al’ada a garin Ozoro mai suna Cif Omorede Sunday, tare da wasu mutane hudu, biyo bayan bayyanar wasu bidiyoyi da ke nuna cin zarafin mata da fyade a yankin Ƙaramar Hukumar Isoko ta Arewa da ke jihar.

Kakakin rundunar, Bright Edafe, ya bayyana a ranar Juma’a, 20 ga Maris, 2026, cewa hotunan bidiyon sun nuna yadda aka keta wa matasa mata haddi da mutunci, wanda hakan ya saba wa doka da hakkin ɗan-adam.

Tuni dai Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Aina Adesola ya bada umarnin gudanar da bincike nan take, wanda ya kai ga kamo babban mai shirya taron da sauran mutanen.

Daga lokacin ne aka mayar da maganar zuwa sashen binciken manyan laifuka na jiha (SCID) domin zurfafa bincike da kamo duk wanda ke da hannu.

Rahotanni sun nuna cewa an kai wa mata da ‘yan mata hari ne yayin wani bikin al’ada da aka gudanar a ranar Alhamis a masarautar Ozoro.

Mazauna yankin sun bayyana taron a matsayin “bikin fyade”, inda ake tsoratar da mata su zauna a gida. Duk macen da aka gani a waje a wannan lokacin tana fuskantar barazanar cin zarafi daga rukunin maza.

•Akwai babban damuwa musamman kan lafiyar daliban jami’ar jihar Delta (DELSU) da ke Ozoro, da kuma baƙi waɗanda ba su san haɗarin da ke tattare da al’adar ba.

A ƙarshe, Kwamishina Adesola ya buƙaci al’umma musamman wadanda aka ci zarafinsu da kuma shaidu, da su fito su ba da bayanai ga ‘yan sanda, yana mai alƙawarin cewa za a sakaya sunayensu kuma za a biya wa kowa haƙƙinsa domin tabbatar da adalci a gare su.

By Babaji