
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Donald Trump na Amurka, ya caccaki ƙasashen mambobin ƙungiyar gamayyar tsaro ta NATO, inda ya bayyana su a matsayin matsorata sakamakon ƙin bayar da goyon baya ga Amurka da Isra’ila a yaƙinsu da ƙasar Iran.
Wannan bayani na Trump na zuwa ne a lokacin da rikicin ke cigaba da durƙusar da tattalin arziƙin duniya, musamman ta fuskar tsadar kayayyakin makamashin man fetur da Iskar Gas saboda ƙamarin rikicin.
Trump ya bayyana matuƙar ɓacin ransa akan yadda ƙasashen Turai suka ja da baya wajen tura dakarunsu ko bayar da tallafin soji, lamarin da ke nuna rashin goyon bayan Washington daga ƙawayenta na Yammacin duniya, kamar yaddaya wallafa a dandalinsa na Truth Social a jiya Juma’a.
Ya ce, ƙasashen NATO ba sa son shiga yaƙin akan Iran, amma kuma suna ƙorafi akan hauhawar farashin makamashi. Hakan na faruwa ne sakamakon iko da Iran ɗin ke da shi na kula da mashigar makamashi ta ruwa da ke yankin Strait Hormuz.
Masana na ganin cewa ƙasashen NATO na fargabar shiga wannan yaƙin ne don gudun kada rikicin ya rusa hanyoyin iskar gas ɗinsu, da kuma tsoron fuskantar hare-haren ramuwar gayya daga dakarun Iran.
