Binance na neman sulhu da Gwamnatin Tarayya kan shari’ar rashin biyan haraji

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kamfanin Binance Holdings Limited da ya shahara da harkar cinikayar kuɗaɗen intanet (cryptocurrency), ya fara tattaunawa da hukumomin Nijeriya domin warware matsalolin shari’ar rashin biyan haraji akansa, matakin da ya dakatar da sauraron ƙarar batun da ke gaban Babbar Kotun Tarayya ta Abuja.

An sanar da haka ne yayin da Mai Shari’a Emeka Nwite nemi a cigaba da sauraron shari’ar, inda ɓangarorin masu kare wanda ake ƙara da na masu gurfanarwa suka tabbatar wa kotun cewa an fara tattaunawa neman sulhu tsakanin kamfanin da kuma gwamnati.

Lauyan da ke kare Binance, Sunday Agaji ya sanar da kotun cewa kamfanin ya fara tattaunawa da hukumomin harajin Nijeriya domin warware matsalolin a wajen shari’a.

Ganin haka ya sa lauyan da ke kare ɓangaren gwamnati, Moses Ideho, wanda mataimakin darakta ne a Hukumar Tattara Haraji ta Ƙasa (NRS), ya ce kamfanin ya nemi hukumar akan batun neman mafita akan al’amarin.

Duk da cewa an shirya cigaba da sauraron shari’ar, kotun ta zaɓi ɗage hukunci a kai domin ba wa ɓangarorin biyu damar tattaunawa akan hanyoyin shawo kan al’amarin.

Akan haka ne Alƙali Nwite ya ɗage zaman shari’ar zuwa ranar 12 ga wata Mayu domin yanke hukunci a kai.

Ana tuhumar Binance ne da laifuka huɗu da suak shafi yin ayyukansa a Nijeriya ba tare da biyan haraji ba.

By Babaji